Buhari Ya Gana da Gwamnan CBN, Shugaban NGF, Bagudu Kan Karancin Naira

Buhari Ya Gana da Gwamnan CBN, Shugaban NGF, Bagudu Kan Karancin Naira

  • Shugaban kasa ya gana da gwamnan CBN, shugaban gwamnoni da Atiku Bagudu kan karancin sabbin takardun naira
  • Abdulrasheed Bawa, shugabn EFCC da shugaban dakarun tsaro na kasa sun halarci taron yau Talata 7 ga watan Fabrairu
  • Idan baku manta ba gwamnonin APC sun zauna da Shugaba Buhari kan batun a ranar 3 ga watan Fabrairu, 2023

Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya sa labule da shugaban ƙungiyar gwamnonin Najeriya, Aminu Tambuwal da shugaban gwamnonin APC, Atiku Bagudu.

Shugaban ƙasan ya zauna da manyan gwamnonin ne kan halin da ake ciki na karancin sabbin takardun naira guda uku da CBN ya canja.

Taron Buhari da manyan jiga-jigai kan sauya naira.
Buhari Ya Gana da Gwamnan CBN, Shugaban NGF, Bagudu Kan Karancin Naira Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Kwamitin yakin neman zaben shugaban ƙasa na jam'iyyar APC (PCC) ya wallafa Hotunan taron a shafinsa na dandalin Tuwita ranar Talata 7 ga watan Fabrairu, 2023.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Shugaban INEC Ya Sa Labule Da Gwamnan CBN Saboda Karancin Takardun Naira

Taron Buhari da masu ruwa da tsaki.
Buhari Ya Gana da Gwamnan CBN, Shugaban NGF, Bagudu Kan Karancin Naira Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sauran kusoshin gwamnati da suka halarci zaman

Sauran manyan jiga-jigan da suka halarci zaman sun haɗa da, gwamnan babban banki CBN, Godwin Emefiele, shugaban hukumar yaƙi da cin hanci (EFCC), Abdulrasheed Bawa.

Haka zalika shugabam dakarun tsaron ƙasar nan, Janar Lucky Irabor, ya halarci taron wanda ya gudana a ofishin shugaban kasa da ke Aso Villa a birnin tarayya Abuja.

Sai dai bayanai sun nuna cewa taron da aka shirya tun asali da ƙungiyar gwamnoni, an soke shi bisa dalilai da har yanzun ba'a bayyana su ba.

Me aka tattauna a wurin ganawar?

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa zuwan gwamna CBN wurin ya nuna alamar cewa an shirya taron ne domin tattauna batutuwan da suka shafi canja takardun kuɗi, wanda a yanzu ya jefa mutane cikin kakanikayi.

Idan baku manta ba, a ranar 3 ga watan Fabrairu, shugaba Buhari ya gana da gwamnonin APC inda wasu daga ciki suka roke shi ya bar tsoho da sabon kuɗi su ci gaba da yawo hannun jama'a.

Kara karanta wannan

Godwin Emefiele Yaudarar Buhari Yayi, Ya Raina Masa Wayau: Adams Oshiomole

A cewarsu, hakan zai rage raɗaɗi da wahalhalun da talakawa ke fuskanta a dukkanin sassan kasar nan sakamakon tsarin sauya takardun naira guda uku.

Wata majiya daga fadar shugaban kasa ta ce Buhari ya nuna damuwa kan yuwuwar take umarnin doka. Babu ɗaya daga mahalarta taron da ya zanta da manema labarai.

Taron Abuja.
Buhari Ya Gana da Gwamnan CBN, Shugaban NGF, Bagudu Kan Karancin Naira Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

A wani labarin kuma kun ji cewa wani Sarki ya sha kunya yayin da ya je banki neman sabbin takardun naira

Basaraken ya je bankin ne tare da mutane masu dumbin yawa a kokarin neman samun sabbin takardun kuɗi ranar Litinin.

Sai dai duk da girmamawar da mutane suka masa na buɗa masa hanya, ma'aikatan bankin ba saurare shi ba ballantana su buɗe masa kofa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel