Masu Sana'ar POS a Jigawa Sun Yaba Wa Babban Bankin Najeriya, CBN

Masu Sana'ar POS a Jigawa Sun Yaba Wa Babban Bankin Najeriya, CBN

  • Gwamnan babban bankin kasa CBN ya kaddamar da shirin raba wa al'ummar karkara sabon kudi a Jigawa ta hannun masu sana'ar POS
  • Masu sana'ar POS din a jihar sun bayyana yadda al'umma suka ji dadin tsarin saboda rage wahalar bin dogon layin banki
  • Babban bankin ya ce anyi hakan ne da nufin saukakawa mutanen karkara wajen samun sababbin kudin

Jigawa - Wasu masu sana'ar POS a Jihar Jigawa sun yabawa kokarin babban bankin kasa CBN kan rarraba musu takardun sababbin Naira don rabawa al'umma a sassan jihar.

Daily Trust a ranar Lahadi ta ruwaito cewa kowanne mai sana'ar POS ya samu N500,000 na sabuwar Naira inda zasu raba N10,000 ga daidaikun mutane.

Jigawa Map
Masu Sana'ar POS a Jigawa Sun Yaba Wa Babban Bankin Najeriya, CBN. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Hukumar yan sanda ta yi magana game da mutumin da ya mutu a layi ciki banki

Shirin bankin ya zagaye kananan hukumomin jihar 27 da nufin saukakawa mutanen karkara wajen samun sababbin kudin.

Wani mai POS, Abubakar Yusuf, ya yabawa babban bankin bisa sahale musu aikin rabon kudin ga al'umma, yana cewa, mutane sunji dadin hakan.

Nura Ibrahim daga karamar hukumar Kiyawa ya ce, ''Duk da dai kudin yayi kadan, mutane sunji dadin N10,000 da suka samu saboda akwai wahala sosai wajen samun kudi a banki saboda dogwayen layi.

Bayan nan, wani mai sana'ar, Adamu Ibrahim daga garin Andaza ya yabawa babban bankin.

Shugaban tawagar babban bankin, Abdul Amadu, ya ce babban bankin ya kirkiri shirin ne don taimaka mutanen karkara da kuma tabbatar da jama'a basu sha wahalar samun sabon kudin ba.

Wakilin Legit.ng a birnin Dutse Jihar Jigawa ya zaga ya tattauna da wasu masu sana'ar na POS domin jin ko su ma sun amfana da wannan tsarin na CBN.

Kara karanta wannan

Assha: Na Kusa Da Buhari Sun Fi Damuwa Da Batun Sauyin Kudi, Minista Ya Bayyana Gaskiyar Abin da Ke Ransa

Wani mai sana'ar POS a sabuwar kasuwa da ke Dutse, da ya nemi a boye sunansa, ya ce shi ya tafi banki amma bai samu kudin ba domin ba kowanne mai na'urar POS ne aka bawa ba.

Kalamansa:

"Sai wadanda POS dinsu daga bankuna suka karba ake ba wa wannan kudin, wasun mu kuma masu amfani POS din Quickteller (Monie Point) ba mu cikin tsarin.
"Abin da muka dogara da shi shine N20,000 da muka iya cire wa daga asusun bankunan mu, ni bankuna uku na ke aiki da su, don haka N60,000 na iya samu."

Hakazalika, wata mai POS din mai suna Hajiya Rabi a Dutse ta ce ita ma gaskiya bata iya samun wannan N500,000 din ba.

Ta ce iya N20,000 a kowanne asusun bankinta da ta ke iya cirewa ta ke amfani da shi, hakan kuma ba ya isan kwastomominta.

Kalamanta:

"Ban samu kudin ba, N20,000 da na ke cirewa daga asusun bankuna a kanta ne na ke amfani da su, muna fatan ganin karshen wannan karancin takardun nairan nan bada dadewa ba."

Kara karanta wannan

Wahala Ta Kare, CBN Ya Ba Da Sabon Umarni Na Yadda Za a Ba 'Yan Najeriya Sabbin Kudi

Ta kara da cewa karancin takardun nairan ya sa ta kara kudin caji da ta ke yi saboda ita ma tana shan bakar wahala kafin ta samu kudin.

Sabbin Naira: Wadanda suka rufe muku kudi za su fito da su, Tinubu

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dan takarar jam'iyyar APC a zaben 2023 ya yi ikirarin wasu suna shirya masa makarmakiya ta hanyar boye sabbin kudi don harzuka al'umma.

Tinubu ya yi wannan zargin ne yayin da ya ke yi wa magoya bayansa jawabi wurin kamfen a Ado Ekiti.

Asali: Legit.ng

Online view pixel