Ka Jefa Talakawa Cikin Wahala: Ka Nemo Hanyar Maganceta: Atiku Ga Emefiele

Ka Jefa Talakawa Cikin Wahala: Ka Nemo Hanyar Maganceta: Atiku Ga Emefiele

  • Atiku ya zama mutum na farko da ya bayyana cewa kada a sake dage wa'adin daina amfani da Naira
  • Saura kwanaki takwas yanzu da ranar 10 ga Febrairu da gwamnan CBN ya sanar karshen makon da ya gabata
  • Gwamnatin shugaba Buhari ta buga sabbin takardun Naira ranar 15 ga Disamba, 2022

Abuja - Dan takara a zaben shugaban kasan Najeriya karkashin jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya yi kira ga bankin CBN kada ya sake dage wa'adin daina amfani da tsaffin takardun Naira.

Atiku, a jawabin da ofishin kamfensa ya fitar ranar Laraba a birnin tarayya Abuja, ya bayyana cewa bankin ya fitar da isassun sabbin kudi cikin al'umma, rahoton ChannelsTV.

Atiku ya jinjinawa CBN kan kara wa'adin da kwanaki goma bisa kiraye-kirayen mutane amma dai a dau matakan tabbatar da an samu isassun kudade cikin al'umma.

Kara karanta wannan

Wa'adin Dena Karbar Tsaffin Naira: Atiku Ya Aika Sako Mai Karfi Ga Gwamnan CBN Emefiele

New Naira
Ka Jefa Talakawa Cikin Wahala: Ka Nemo Hanyar Maganceta: Atiku Ga Emefiele
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tsohon mataimakin shugaban kasan ya bada shawaran cewa kada a sake dage wa'adin daga 10 ga Febrairu saboda idan akayi haka, ba'a cimma manufar sauya fasalin Naira ba.

A cewarsa:

"Cikin wadannan kwanaki goma, ina kira ga CBN ta samar da hanyoyin magance matsalolin da mutane ke fuskanta wajen canza tsaffin kudadensu zuwa sabbi."
"Muna ba CBN shawara su kara buga sabbin kudade domin kawar da karancin da ake samu cikin talakawa, musamman mazauna karkara masu bukatar kudn don harkokin yau da kullum."
"Hakazalika CBN ta maida hankali kan wasu manya masu kuka suna bukatar a sake dage wa'adin tsaffin Naira saboda suna da wata manufa mara kyau."
"Ko shakka babu ina goyon bayan gina tattalin arzikin da za'a waye gari kowa na amfani da hanyoyi zaman wajen kasuwanci da kuma rage yawan takardun Naira cikin al'umma."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Hadimar Gwamna Tambuwal Ta Mutu Sakamakon Cinkoso Lokacin Kamfen Atiku a Sokoto

2023: Tsohon Minista Ya Tona Wasu Mutane a Fadar Shugaban Kasa Dake Tare da Atiku

Daraktan sabbin kafafen yada labarai na kwamitin kamfen Tinibu/Shettima, Femi Fani-Kayode, ya yi ikirarin cewa akwai wasu mutane a fadar shugaban kasa dake wa Atiku Abubakar aiki.

Fani-Kayode ya yi wannan furucin ne yayin hira a gidan talabijin Channels tv a shirinsu mai suna Politics Today sa'ilin da yake tsokacin kan kalaman gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai

Asali: Legit.ng

Online view pixel