Kwankwaso Ya Wanki Kafa Zuwa Nijar Don Tallata Aniyarsa Ta Gaje Buhari a Zaben 2023

Kwankwaso Ya Wanki Kafa Zuwa Nijar Don Tallata Aniyarsa Ta Gaje Buhari a Zaben 2023

  • Dan takarar shugaban kasa a NNPP ya wanke kafa zuwa Nijar don neman goyon bayan jama’ar kasar da ‘yan Najeriya mazauna can
  • Kwankwaso ya gana da shugabannin kasar don neman shawari da tattauna batutuwan tsaro, tattalin arziki da fasaha a Afrika
  • Kwankwaso na da burin gaje kujerar Buhari a zaben bana, ya ce shine zai iya gyara Najeriya ta hau saitin da ake so

FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa a jam’iyya mai alamar kayan marmari ta NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya shilla tallata aniyarsa ta gaje Buhari zuwa jamhuriyar Nijar mai makwabtaka da Najeriya.

Ya shaidawa wadanda suka tarbe shi a Nijar, ‘yan kasar da kuma ‘yan Najeriya mazauna can cewa, zai kawo tsarin alakar kasashen Afrika ta Yamma ta fannin tsaro, shugabanci, fasaha da tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa Sun Aikawa Shugaban Kasa Buhari Muhimmin Sako a Kan Shirin Zabe

Wannan batu na fitowa ne daga wata sanarwa da ya fitar a Abuja ta hannun Ladipo Johnson, kakakin tawagar gangamin kamfen Kwankwaso/NNPP, Punch ta ruwaito.

Kwankwaso ya je tallata kansa a jamhuriyar Nijar
Kwankwaso Ya Wanki Kafa Zuwa Nijar Don Tallata Aniyarsa Ta Gaje Buhari a Zaben 2023 | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Dalilin zuwan Kwankwaso Nijar

Ya bayyana cewa, ziyarar Kwankwaso a Nijar na daga cikin kokarinsa na neman shawari da kulla alaka da masu ruwa da tsaki da kasashe makwabtan Najeriya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hakazalika, ya ce irin wannan ziyara za ta taimaka wajen gano hanyoyin kullawa da kawo sabbin ka’idojin kasashen waje ga ‘yan Najeriya mazauna waje.

A bangare guda, Kwankwaso ya kai ziyara ga shugaban jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum, inda suka yi tattaunawa mai zurfi.

Sanarwar da NNPP ta fitar ta ce, sun tattauna game ‘yan Najeriya mazauna Nijar da dai sauran batutuwa ci gaban kasashen biyu.

Ya gana da tsohon shugaban Nijar

Hakazalika, ya ziyarci tsohon shugaban jamhuriyar ta Nijar, Mahamadou Issoufou don neman goyon baya da shawari, Business Day ta tattaro.

Kara karanta wannan

Idan Ya Ci Zabe, Atiku Ya Bayyana Abin da Zai Yi Kafin Ya Cika Watanni 6 a Kan Mulki

Kwankwaso na daya daga cikin ‘yan takarar da ke son gaje kujerar Buhari, ya kuma yi imanin zai kawo sauyi mai kyau ga kasar idan aka zabe shi.

Shugaban NNPP ya koma APC a Gombe

A bangare guda a gida Najeriya, Kwankwaso ya yi rashin shugaban jam'iyyar NNPP na jihar Gombe, wanda ya koma tsagin gwamnan APC, Inuwa Yahaya.

An ce Abdullahi Maikano Umar ya gana da gwamnan jihar Gombe, sun tattauna kana ya bayyana ficewa daga NNPP.

Kwankwaso na samun koma baya a bangaren magoya baya yayin da zaben 2023 ke kara gabatowa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel