Shugaban NNPP Na Gombe, Maikano Ya Fice Daga Jam’iyyar APC, Ya Gana da Gwamna Inuwa

Shugaban NNPP Na Gombe, Maikano Ya Fice Daga Jam’iyyar APC, Ya Gana da Gwamna Inuwa

  • Yayin da zaben shugaban kasa ya gama karatowa, shugaban jam'iyyar NNPP a jihar Gombe ya saki tafiyar su Rabiu Kwankwaso
  • Abdullahi Maikano Umar ya ce ya koma jam'iyyar APC bayan ganawa da gwamnan jihar, Muhammadu Inuwa Yahaya
  • A baya shugaba jam'iyyar a yankin Arewa maso Gabas ya bayyana sauya sheka zuwa PDP tare da marawa Atiku Abubakar baya

Jihar Gombe - Shugaban jam'iyyar NNPP na jihar Gombe, Abdullahi Maikano Umar ya bayyana sauya sheka zuwa jam'iyyar NNPP, Tribune Online ta ruwaito.

An ruwaito cewa, Maikano ya bayyana barin NNPP bayan wata ganawa da ya yi da gwamnan jihar, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya a ranar Alhamis 2 ga watan Fabrairu da yamma.

Ya zuwa yanzu dai babu wasu bayanai da aka samu game da ganawar gwamnan da tsohon shugaban na NNPP, amma dai wannan babban ci gaba ne da gwamnan da ke neman a sake zabensa a jihar.

Kara karanta wannan

Kuyi Hakuri Da Wahalar Karancin Naira Kamar Yadda Kuke Hakuri Da Shan Magani Idan Baku Da Lafiya: Ministar Kudi

Shugaban NNPP a Gombe ya koma APC
Shugaban NNPP Na Gombe, Maikano Ya Fice Daga Jam’iyyar APC, Ya Gana da Gwamna Inuwa | Hoto: tribuneonlineng.com
Asali: UGC

Idan baku manta ba, da raguwar mambobi na baya-bayan nan a NNPP ya maida jam'iyyar ta zama ta marasa rinjaye a majalisar dokokin jihar Gombe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har yanzu jam'iyyar NNPP bata yi martani ga wannan rashi da ta yi na babban jigo kuma mai tallata ta jihar Arewa maso Gabas ba.

Shugaban NNPP na yankin Arewa maso Gabas ya sauya sheka

A baya kadan, shugaban NNPP a yankin Arewa maso Gabas ya bayyana sauya sheka daga jam'iyyar zuwa PDP, inda ya marawa Atiku Abubakar baya, Leadership ta ruwaito.

Dr. Babayo Liman ya bayyana kara cewa, ya bar NNPP ne tare da miliyoyin mambobin da suka gaji da zama a jam'iyyar da yace ta gaza yin gaba balle baya.

Da yake jawabi ga manema labarai a jihar Bauchi, Babayo ya ce akwai mambobi sama da miliyan 2.8 da suka bar jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnonin APC Zasu Shiga Ganawar Sirri Da Buhari Kan Lamarin Naira Da Tsadar Mai

Wannan dai ba karamar barazana bace ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar, Rabiu Musa Kwankwaso ba, kasancewar ya ta'allaka rai a samun kur'iun mutanen Arewa.

Saura kwanaki akalla 22 a yi zaben shugaban kasa a Najeriya, ana ci gaba da ganin sauyin sheka daga jam'iyyu da yawa na kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel