Mutumin Ya Yanke Jiki Ya Fadi Matacce a Banki Katin ATM Yaje Karba, Hukumar Yan Sanda

Mutumin Ya Yanke Jiki Ya Fadi Matacce a Banki Katin ATM Yaje Karba, Hukumar Yan Sanda

  • Yan Najeriya na cigaba da fama da wahalar karancin takardun Naira a karkara da birane
  • Wani dan jihar Delta yace ga garinku bayan kwashe sa'o'i yana layi don iya cire kudinsa
  • Kakakin hukumar yan sandan jihar ya ce katin ATM mutumin yaje karba amma lokacinsa yayi

Delta - Wani kwastoman banki ya yanke jiki ya fadi matacce cikin harabar wani banki bayan kwashe awanni kan layi a garin Agbor na jihar Delta.

Wannan abu ya auku ne ranar Alhamis, 2 ga watan Febrairu, 2023 a karamar hukumar Ika ta kudu, rahoton Tribune.

Banki
Wani Mutumi Ya Yanke Jiki Ya Fadi Matacce a Banki Bayan Kwashe Awanni Yana Tsaye a Layi Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Kakakin hukumar yan sandan jihar Delta, DSP Bright Edafe, ya tabbatar da aukuwan wannan lamari.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Jan aiki: Daga lika sabbin Naira a gidan biki, EFCC ta kama wata fitacciyar 'yar fim

DSP Bright Edafe ya ce mutumin ya shiga bankin karban katin ATM dinsa ne.

A cewarsa:

"Labarin dake yawo cewa wani mutumi ya yanke jiki ya fadi matacce yayin kokarin cire kudi ba an yi karin gishiri cikin miya. Ya yanke jiki ya fadi ne yayin layin karban sabon katin ATM."

Fusatattun matasa sun kai hari ofishin gwamna yayin zanga-zanga

Mumunar zanga-zanga ta barke a Ibadan, babbar birnin jihar Oyo sakamakon halin kunci, tsadar kaya, da kuma rashin takardun Nairan siya a Najeriya.

Hotuna da bidiyoyi sun nuna yadda fusatattun matasa sun tare hanyoyi suna kone-konen tayoyi.

TheNation ta ruwaito cewa matasan sun kai hari ofishin gwamnan jihar, Seyi Makinde.

Har direbobin motocin haya ba'a bari a baya ba wajen zanga-zangar.

Shugaba Buhari Yace 'Yan Najeriya su Basi Kwana 7 don Magance Matsalar Sabbin Kudi

Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci 'yan Najeriya da su bashi kwanaki bakwai kacal domin ya shawo kan matsalolin da suka kawo karancin sabbin takardun kudi.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan Bindiga Sun Budewa Dan Takaran Gwamnan Jihar Ebonyi Wuta, An Kashe Direbansa

Shugaban kasan yace ya ga rahotanni da ke nuna karanci da kuma illar da rashin kudin ya janyowa kasuwanci da jama'a talakawa.

Yace ragowar kwanaki bakwai daga cikin goma da aka kara kan wa'adin amfani da sabbin kudin za a yi su ne ana shawo kan matsalolin da suka hana nasarar tabbatar da tsarikan sabbin kudin.

"Zan koma kan babban bankin Najeriya da kamfanin buga kudi. Za a yanke hukunci a cikin ragowar kwanaki bakwan nan da aka kara."

- Shugaban kasan ya tabbatar a ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel