Yan Bindiga Sun Tafi Gidan Dan Takarar Majalisa A Kaduna, Sun Kashe Mutum 2

Yan Bindiga Sun Tafi Gidan Dan Takarar Majalisa A Kaduna, Sun Kashe Mutum 2

  • Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hari gidan dan takarar majalisa na jam'iyyar LP a Lere, Suleiman Tambaya
  • Maharan sun tafi gidan Tambaya ne da ke kauyen Gure a daren ranar Juma'a suna nemansa amma ba su same shi ba
  • Yayin harin, yan bindigan sun harbi mutane guda biyu, dayansu ya rasu nan take dayan kuma ya rasu bayan an kai shi asibiti

Kaduna - Yan bindiga sun kai wa dan takarar majalisar tarayya na Lere a jihar Kaduna, Suleiman Tambaya, a daren ranar Juma'a na nufin kashe shi a gidansa kauyen Gure da ke karamar hukumar Lere.

Dan takarar majalsar ya tallake rijiya da baya amma maharan sun halaka mutane biyu kamar yadda The Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Sauya Naira: "Atiku Baya Kaunar Talakawan Najeriya," El-Rufai Ya Ragargaji Dan Takarar Shugaban Kasa Na PDP

Kaduna Map
Yan Bindiga Sun Tafi Gidan Dan Takarar Majalisa A Kaduna, Sun Kashe Mutum 2. Hoto: @ChannelsTV
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lamarin ya faru ne misalin karfe 10 na dare a lokacin da dan takarar majalisar ke hanyarsa na zuwa taron siyasa a Kaduna, babban birnin jihar.

Tambaya ya magantu kan harin

Da ya ke magana da wakilin Punch kan harin a ranar Asabar, Tambaya ya ce idan ba domin ikon Allah ba da kuma mutanen yankin da yan bijilante, da wani labarin ake yi a yanzu.

Ya ce yan sanda a Lere sun amsa kirar neman dauki.

Tambaya ya ce:

"Ina shirin zuwa gida ne a ranar Juma'a amma na yi magana da dan takarar gwamnan mu kuma ya ce in taho in gan shi. Hakan yasa na juya zuwa Kaduna.
"Misalin karfe 10 na daren ranar Juma'a, wasu yan bindiga su bakwai sun taho gida na da ke kauye (Gure), suna tambayar ina nake domin ya kamata ina gida.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Yan Bindiga Sun Bude Wa Ayarin Motoccin Dan Takarar Gwamna Wuta, Sun Bindige Direbansa

"Wasu matasa a gida na sun iya tserewa sun sanar da mutanen garin kuma yan bijilante suka taho suka yi artabu da su. A yayin hakan sun kashe mana yara biyu.
"Ka san garin suna da bijilante kuma nan take suka taho, yan bindigan sun harbe yaran mu biyu. Daya ya mutu nan take dayan kuma sai da aka kai shi asibiti ya rasu.
"Mun kai wa yan sanda rahoto kuma sun zo nan take zuwa inda abin ya faru."

Martanin yan sanda

Kawo yanzu rundunar yan sanda ba ta ce komai kan lamarin ba ko gwamnatin jiha.

Da aka tuntube shi a wayar tarho, kakakin yan sandan jihar DSP Mohammed Jalige, bai amsa waya ba ko sakon tes.

Yan bindiga sun kai wa tawagar dan takarar shugaban kasa na LP hari a hanyar zuwa kamfen

A wani rahoton, kun ji cewa wasu mahara sun kai wa tawagar Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour hari a Katsina.

Kara karanta wannan

Na Rantse Ba Wanda Muke Tsoro A Kasar Nan, El-Rufa'i Ya Mayarwa Fulogan Buhari Martani

A wani jawabi da Diran Onifade ya fitar, dan takarar shugaban kasar ya yi tir da harin da aka kai masa shi da mutanensa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel