Sauya Naira: "Atiku Baya Kaunar Talakawan Najeriya," El-Rufai Ya Ragargaji Dan Takarar Shugaban Kasa Na PDP

Sauya Naira: "Atiku Baya Kaunar Talakawan Najeriya," El-Rufai Ya Ragargaji Dan Takarar Shugaban Kasa Na PDP

  • Malam Nasir El-Rufai, gwamnan Jihar Kaduna, ya gargadi yan Najeriya su yi takatsantsan da Atiku Abubakar
  • El-Rufai wanda ya rike mukamin ministan Abuja a lokacin da Atiku ke mataimakin shugaban kasa, ya ce dan takarar shugaban kasar na PDP ba ya kaunar talakawan Najeriya
  • Gwamnan na Jihar Kaduna ya yi wannan furucin ne a matsayin martani kan matsayar Atiku game da sauyin fasalin kudi na CBN

FCT, Abuja - Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya ce ra'ayin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar kan dokokin sauya tsaffin kudi don karban sabbi na CBN ya nuna cewa shi mugu ne kuma bai damu da talakawa ba.

El-Rufai ya ce bukatar cewa kada CBN ta tsawaita wa'adin dena karbar tsaffin nairan bayan ranar Juma'a 10 ga watan Fabrairu, ya tabbatar cewa dan takarar shugaban kasar na PDP bai damu ko bai tausayin masu karamin karfi ba a kasar, wadanda su abin ya fi shafa.

Kara karanta wannan

Magana ta Fara Fitowa: El-Rufai Ya Yi Karin Haske Kan Manyan da ke Yakar Takarar Tinubu

Gwamnan Kaduna El-Rufai
Sauya Naira: "Atiku Baya Kaunar Talakawan Najeriya," El-Rufai Ya Ragargaji Dan Takarar Shugaban Kasa Na PDP. Hoto: Gwamnatin Kaduna
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da ya ke magana a TVC a ranar Alhamis, 2 ga watan Fabrairu, gwamnan na Kaduna ya ce:

"Idan ka kalli jawabi daga dayar jam'iyyar bayan na yi magana kan sauya kudi, ba adawa da tsarin muke yi ba. Rage amfani da takardan naira abu ne mai kyau. Ba mu da matsala da shi, amma ba zai yiwu ka yi shi cikin yan makonni ba.
"Ka bawa kowanne manomi, tireda, dalibi, yan kasuwa da ke kauyuka damar zuwa banki su sami sabbin kudin ko ka tafi ka tarar da su inda suke kasuwancinsu. Mu zauna mu duba abin mu bada lokacin da ya dace."

A kan kin amincewa da shawarar Atiku na kada a tsawaita wa'adin, El-Rufai ya ce:

"Duba da cewa dan takarar shugaban kasar na PDP a makon da ta gabata ya nemi a tsawaita yanzu kuma kwatsam ya fara rera wata wakar abin tambaya ne. Yana son yin magana ne don saba wa jam'iyyar mu da shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Karina Bayani: Gwamnonin APC Sun Roki Buhari Ya Bari a Dinga Amfani da Tsofaffi da Sabbin Kudi

"Yanzu bayan karin kwana 10, ya juya ya ce kada CBN ta kara wa'adin na nufin wani abu. Ya nuna karara cewa yana jin dadin wahalan da yan Najeriya ke ciki a yanzu.
"Na ga zanga-zanga a Legas yau. Akwai rahotanni cewa mutane ba su iya siyan abinci a Kaduna; saboda babu kudi amma dan takarar shugaban kasar na PDP ya ce kada a tsawaita saboda yana amfana da abin."

Ya ce Atiku na fata zai amfana da wahalar da yan Najeriya ke ciki saboda tsarin.

Ya kara da cewa:

"Ina so yan Najeriya su fahimci karara cewa abin takaici ne a ce wani da ya nemi a tsawaita wa'adin makon jiya yanzu yana cewa kar a kara. Idan yana da tausayin talaka, manoma, yan kasuwa mata da maza, yan kauye, a zuciyarsa ba zai ce haka ba."

2023: Arewa ba ta da uzurin rashin zaben Bola Tinubu, Gwamna Ganduje

Kara karanta wannan

Da Gaske Buhari Ya So Ahmad Lawan Ya Maye Gurbinsa? El-Rufai Ya Warware Abun da Buhari Ya Fada Masu

Dakta Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan Kano ya ce al'ummar arewa ba su da wani uzurin rashin zaben dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Tinubu a 2023.

Ganduje ya ce Tinubu ya taka rawar azo a gani wurin ganin cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya dare kan mulki, don haka lokaci ya yi da za a masa sakayya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel