'N300b CBN ta Buga Bayan Tattara N2trn na Tsofaffin Kudi' Gwamnonin APC Sun Bayyana Halin da Talakawa ke Ciki

'N300b CBN ta Buga Bayan Tattara N2trn na Tsofaffin Kudi' Gwamnonin APC Sun Bayyana Halin da Talakawa ke Ciki

  • Gwamna Nasir El-Rufai na jihar kaduna yace Gwamnonin APc sun roki Buhari kan a dinga amfani da tsofaffi da sabbin takardun naira
  • Yace CBN ta buga N300 biliyan bayan ta tattara N2 tiriliyan daga hannun mutane, wanda hakan yasa dole aka fada halin da ake ciki
  • Ya koka kan yadda talakawa suka fada wani hali yayin da 'yan kasuwa ke ta tafka asara saboda rashin masu siyan kayansu

FCT, Abuja - Gwamnonin jam'iyyar APC sun roki shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya bari a dinga amfani da sabbin takardun Naira da tsofaffin domin saukakawa 'yan Najeriya.

Buhari da Gwamnonin APC
Gwamnonin APC sun Mika Muhimmiyar Bukata 1 Gaban Buhari kan Musayar Sabbin Kudi. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, yace wannan bukatar an mika ta ne gaban Shugaban kasa yayin da gwamnonin APC suka gana da shi a ranar Juma'a, jaridar The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Buhari Ya Bayyana 'Yan Najeriya Kwanakin da Za a Kwashe Kafin Matsalar Sabbin Kudi Tazo Karshe

Gwamnan jihar Kadunan yace shugaban kasan bai yi watsi da bukatar ba kuma bai bayyana amincewarsa a kan ta ba.

El-Rufai na tare da Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, yayin da ya zanta da manema labarai kan abinda aka tattaunaa taron da aka yi a gidan gwamnati.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yace duk da babban bankin Najeriya na CBN ya samu nasarar tattara N2 tiriliyan na tsofaffin kudin da ka yawo a gari, N300 biliyan kadai na sabbin kudin suka buga.

Gwamnan yace idan babban bankin na Najeriya ya yi niyyar tabbatar da tsarikan amfani da kudi ba tsaba ba, babban bankin ya dace ya buga a kalla rabin yawan kudin da suka tattara.

Yace gwamnonin sun sanar da shugaban kasa cewa talakawa ne ke azabtuwa sannan 'yan kasuwa na ta tafka asarar kayayyaki saboda rashin masu siya.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Zance ya kare, kotu ta fadi wanda zai yi takarar gwamna a PDP a jihar Taraba

El-Rufai yayi kira ga Buhari da ya sake duba matsayarsa a wannan batun.

Gwamnan ya kara da cewa, shugaban kasan bai amince ko watsi da wannan bukatar da suka mika gabansa ba.

Yace Atiku Bagudu, Gwamnan jihar Kebbi kuma shugaban zauren gwamnonin APC yana ganawa na sirri da shugaban kasa duk a kokarinsu na ganin an samu maslaha kan lamarin.

Shugaba Buhari yace nan da kwanaki 7 matsalar karancin kudi zai zama tarihi

A wani labari na daban, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa 'yan Najeriya su bashi kwanaki bakwai kacal, zai magance matsalar karancin kudi da ya addabesu.

Ya sanar da cewa, ya ga rahotanni kan halin da kasuwanci da jama'a suka fada, kuma kafin nan da ranar 10 ga Fabrairu na cikar wa'adin da ya bada, za a samu isassun kudi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel