Yadda Ma'aikatan Banki ke Siya Mana da Sabbin Takardun Naira, Mai POS Yayi Fallasa

Yadda Ma'aikatan Banki ke Siya Mana da Sabbin Takardun Naira, Mai POS Yayi Fallasa

  • Yayin da al'umma sule Allah wadai da halin masu na'urar cire kudi (POS) kam yadda suke amsar makudan kudade don ba da kudi, sun warware zare da abawa
  • Masu sana'ar POS sun fayyace yadda ma'aikatan bankuna ke siyar musu kudi kan farashi mai tsada kafin samun damar mallakar kudin
  • Hakan ya tilasta su fanshe karin kudin ga kwastomominsu, inda suka yi kira ga babban bankin Najeriya (CBN) da ya hukunta duk bankin da ya kama yana mummunar harkallar don ceto 'yan kasa daga kangi

Wasu masu na'urorin cire kudi (POS) sun yi ikirarin cewa wasu jami'an banki su na siyar musu kudi (sabbi da tsoffi).

Masu POS
Yadda Ma'aikatan Banki ke Siya Mana da Sabbin Takardun Naira, Mai POS Yayi Fallasa. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

A tattaunawa daban-daban da NAN a Abuja ranar Juma'a, wasu daga cikin masu na'urorin cire kudin sun bayyana yadda suke biyan makudan kudade don siyan kudi wanda ya danganta da yawan kudin da suka cire.

Kara karanta wannan

Wahala Ta Kare, CBN Ya Ba Da Sabon Umarni Na Yadda Za a Ba 'Yan Najeriya Sabbin Kudi

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Don fanshe karin kudin da aka kara musu, sun labarta yadda basu da wani zabi da ya wuce su kara kudin da suke amsa daga kwastomomi, jaridar The Cable ta rahoto

Haka zalika, sun roki Babban Bankin Najeriya (CBN) da ya hukunta bankunan da suke harkallar.

Wata mai na'urar cire kudi wurin titin Nyanya zuwa NNPC, wacce ta bukaci a sakaya sunanta, ta ce tana biyan karin kudi don cigaba da ganin kasuwancinta na tafiya.

A cewarta:

"Ina biyan makudan kudade don samun wannan kudin da nake ba kwastomomi. Idan ka kalli can, sauran masu POS ba su fito ba.
"Matar (ma'aikaciyar banki) da nake amsar kudin daga wurinta ta daga farashin kudin yau saboda a cewarta kudi na wahala, kuma ta aje min ne don na kirata da wuri.

Kara karanta wannan

Samun wuri: Matar da ta gawurta wajen siyar da Nara ta kare a hannun ICPC, an gano masu bata kudi

"Ina biyan kudi wanda ya danganta da yawan da zan amsa. Wani lokaci, ina biyan N5,000 don amsar N50,000 zuwa N70,000 da nake amsa daga wurinta.
"Ina amsar N500 a duk N5,000 da aka cire da N1000 a duk N10,000 da aka cire a wurin don in fanshe abun da na kashe wajen amsar kudin."

Har ila yau yayin jawabi, Nnedi Ikonye, wata mai POS wuraren Lugbe, ta ce tana biyan N3,000 don cire N65,000 a banki.

"Ana bukatar in bada N3,000 don amsar N65,000 da na cire daga banki, hakan ma don na san wani a bankin ne.
"Hakan ba komai bane kan yadda abokan aiki na suke biya. Suna biyan sama da haka saboda basu san kowa ba a banki."

- Ikonye tace.

Alphonsus Idah, wani mai na'urar cire kudi a kasuwar Mararaba, ya bukaci CBN da ta wajabta tara ga duk bankin da ke siyar da kudi ga kwastomominsu.

Kara karanta wannan

Sabon salo: 'Yan jihar Arewa sun koma amfani da kudin wata kasa a madadin Naira

Wannan, kamar yadda ya yi bayani, zai kawo karshen tsananin rayuwar da 'yan kasa ke ciki.

Wani mai POS, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce ma'aikatan banki na cire kudi ga kwastomominsu.

"A wasu bankuna, ATM ba sa aiki duk da ana zuba kudi.
"Bayan tashi daga aiki, ma'aikatan banki na dawowa don kunna injinan suyi layi don cire kudi.
"Abun takaici shi ne wani ma'aikacin banki zai iya rike katin cire kudi daban-daban kamar 10 sannan ya cire kudi da dukkansu. Wannan abun ban haushi ne."

- A cewar mai na'urar POS din.

Don shawo kan dogon layin a injinan bada kudi (ATMs), CBN ta umarci bankuna da su biya sabbin kudi a bayan kanta, a kullum ga mutum daya N20,000.

Wakiliyar Legit.ng Hausa da ke garin Kano ta zanta da jama'a kan yadda rashin kudi ya addabesu saboda musayar kudin nan da ake yi.

Kara karanta wannan

Yadda ‘Yan ‘Yahoo Suka Damfari Tsohuwa, Suka Sace Duka Dukiyar da ta Mallaka

Wakiliyar ta zagaya POS sama da 10 a ranar Juma'a amma da N2000 ta tsira da kyar shi ma. Ta kuma biya N200 na cajin mai POS din wacce tace duk N1000 tana karbar N100 ne.

Wata matar aure kuwa da ta bukaci a sakaya sunanta a garin Zaria, ta sanar da Legit.ng Hausa cewa a ranar Talata da ta gabata sai bayan isah'i ta daura abinci saboda rashin mahadin girki.

"Maigidana ya je POS sama da 10 amma bai samo mana kudin cefane ba. Ina da komai na girki, kayan miya da nama ne suka gagare ni. Na dafa shinkafa na dinga jiran shi.
"Bayan isha'i wani mai POS da ya tausaya masa saboda dattijo ne, ya kira shi yace ya zo ya karba N5,000. Da wannan kudin muka samu na siya kayan miya na hanzarta nayi miyar da muka ci abincin dare.
"Allah dai ya kawo mana sauki wannan al'amari."

Kara karanta wannan

Wa’adin CBN: Mutanen Karkara Sun Koma Cinikin Bani Gishiri Na Baka Manda Yayin da Sauya Kudi Ke Huta Wutan Yunwa a Gari

- Tace.

Gwamnonin APC sun bukaci Buhari ya bari a dinga karbar sabbi da tsofaffin kudi

A wani labari na daban, Gwamnonin APc suna gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari kan matsalar karancin takardun kudi.

Sun rokesa da ya bari a dinga karbar tsofaffi da sababbin takardun Naira da aka canza a kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel