An Dawo Zaman Da: Mutanen Kauye Sun Daina Amfani Da Kudi, Sun Tsiro Da Hanyar Cinikayya

An Dawo Zaman Da: Mutanen Kauye Sun Daina Amfani Da Kudi, Sun Tsiro Da Hanyar Cinikayya

  • Sabon tsarin CBN da wa'adinsa kan tsoffin kudi na yin tasiri sosai a kan wasu garuruwan karkara a fadin Najeriya
  • Yayin da al'ummar kasar ke fafutukar samun sabbin kudi, kasuwanci da dama na fuskantar kalubale yayin da wasu garuruwa a Benue suka koma cinikayya irin na da
  • A wasu wuraren, farashin kayayyaki ya ninka duk da karin wa'adin daina karbar kudin da CBN ya yi

Benue - Wa'adin daina karbar tsoffin kudi da fara amfani da sabbi ya haifar da gagarumin tashin hankali a garuruwan karkara a fadin kasar nan, musamman a ranar Lahadi, 29 ga watan Janairu.

A ranar 25 ga watan Janairu, garuruwan karkara a jihar Benue da yankunan kudu maso gabas sun daina karbar tsoffin naira a matsayin halastaccen kudi.

Yawancinsu sun dauki kudadensu zuwa banki yayin da wasu suka siya kayayyakin da za su iya siyarwa idan sabbin kudin suka karade gari.

Kara karanta wannan

Borno: ISWAP Sun Yi Rabon Tsofaffin Kudi ga Fasinjojin Motocin Haya Kyauta, Sun ce SU je Bankuna Su Canza su

Jama'a da jarkokin burkutu
An Dawo Zaman Da: Mutanen Kauye Sun Daina Amfani Da Kudi, Sun Tsiro Da Hanyar Cinikayya
Asali: Original

An sha wahala sosai wajen hada-hadar kudi yayin bikin binne wani bawan Allah a Ehuhu-Owkpa da ke karamar hukumar Ogbadibo ta jihar Benue.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lokacin da Legit.ng ta ziyarci wajen binne gawar, yan uwan mamacin sun koka cewa sun wahala wajen gudanar da harkokin binne shin yadda ya kamata saboda karancin sabbin kudi.

Wani dan uwansa mai suna Dave ya ce:

“Yanzu babu abun da Za ka iya yi daidai da tsoffin kudin saboda mutanenmu sun fara daina karbar tsoffin kudin. Kawai muna ta fafutukar ganin mun gama jana’izar dan uwanmu ne.
“Ba Za ka iya siyan komai ba a nan da tsoffin kudin kuma ba Za ka iya tura masu ba saboda masu POS yan kadan da ake da su basu da sabbin kudi. Yawancin yan kauyen na basu da asusun banki, don haka ba Za ka iya tura masu kudin ba. Kusan a matse muke, amma wannan baya nufin cewa bana godiya ga kokarin gwamnati wajen shafe tsoffin kudin.”

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama ainihin mutanen da ke boye sabbin kudi, suna siyarwa a boye a Arewa

Legit.ng ta lura cewa tsoffi maza da mata a garin na ta tunkarar yan birni don sauya kudaden. Amma su kansu wadanda suka zo daga birnin yan kadan ne a hannunsu kuma suna ta taka-tsantsan da sauya kudadensu. Haka kuma ba su tabbatar da ko za a kara wa’adi ko kuma za su iya komawa Abuja kafin cikar wa’adin.

Ku tuna cewa bayan an kai ruwa tana, CBN ya yarda da kara kwanaki 10 kan wa’adin 31 ga watan Janairu da ya fara bayarwa don hada kan kudaden da kyau.

Wannan ya zo ne a ranar Lahadi bayan hankula sun tashi a fadin kasar.

Masu siyar da burkutu sun yi kwantai

Masu siyar da burkutu ma sun hadu da cikas a garuruwan Owukpa da Orokam da ke karamar hukumar Ogbadibo ta jihar Benue saboda rashin sabbin kudi a gari da wa’adin CBN.

A ranar Lahadi, a kasuwar burkutu na Orokom, an gano masu siyar da burkutu suna kin karbar tsoffin naira kuma babu sabo a gari.

Kara karanta wannan

Sabon tsari: CBN ya yiwa mutanen kauye abu daya game da sabbin Naira, sun mika godiya

Da wakilinmu ya tuntubi masu siyarwar da tsoffin kudi, sun ki karba sannan sun gwammaci su siyan da araha idan Za su samu sabbin kudin. An siyar da galan din burkutu da ake siyarwa N4000 kan N2500.

Yawancin dilallan burkutun sun ce ba za su siya ba saboda basu da tsabar kudin biya.

Sai dai wani Matthew Anthony ya fadama Legit.ng cewa karancin sabbin kudin ya karya farashin kayan a kasuwa, yana mai cewa ba burkutu kawai abun ya shafa ba harda sauran kayayyaki a kasuwa.

Muna iya komawa tsarin cinikayya na da - Shugaban Kungiyar, Ojile

Da yake zantawa da Legit.ng a Ukwo Orokam, Shugaban kungiyar Orokam United, Hon. Ojile Onuh ya ce garin na goyon bayan komawa ga cinikayyan da na ‘ban gishiri na baka manda’ kasancewar mutanen garin na wahalar samun kudi.

Ya ce sun dawo gida Don bukukuwan binne-binnen jama’a, bukukuwan aure da sauransu amma sun gaza siyan komai saboda rashin kudi.

Kara karanta wannan

Saura ranar aiki 1 kacal, CBN Tace Ta Fitar Da Sabbin Kudi N120m Jihar Katsina

Ya ce abubuwa sun yi wuya saboda babu sabbin kudi a gari kuma mutane basa karbar tsoffin saboda wa’adin da CBN ya bayar.

Har ila yau, ya ce idan har abun ya ci gaba basu da wani zabi da ya wuce komawa ga cinikayyan da.

A wani labari na daban, wani dan Najeriya ya yi kumfar baki yayin da ya isa banki da tsoffin kudadensa amma mai gadi ya hana shi shiga ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel