Yanzu Yanzu: CBN Ya Umurci Bankuna Da Su Fara Biyan Sabbin Kudi a Kanta

Yanzu Yanzu: CBN Ya Umurci Bankuna Da Su Fara Biyan Sabbin Kudi a Kanta

  • Gwamnan bankin CBN ya umurci bankuna da su fara biyan yan Najeriya sabbin kudi a kan kanta
  • Don ragewa al'ummar kasar radadin halin da suke ciki a yanzu na rashin isasshen kudi a gari, Godwin Emefiele ya bukaci bankuna ta dunga biyansu a kanta
  • Emefiele ya kuma ce an dauki wannan matakin ne don rage yawan layi a akwatunan ATM a fadin Najeriya

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya umurci bankunan kasuwanci da su fara biyan kwastamomi sabbin kudi da aka sauya a kan kanta, jaridar TheCable ta rahoto.

A wata sanarwa da ya saki a ranar Alhamis, 2 ga watan Fabrairu, gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya bayyana cewa an bayar da sabon umurnin ne domin rage kalubalen da yan Najeriya ke fuskanta wajen mallakar sabbin kudin.

Kara karanta wannan

Toh fa: Ba a isa a hana mu sabbin kudi ba, talaka ne mai shan wahala, inji Kwankwaso

Godwin Emefiele
Yanzu Yanzu: CBN Ya Umurci Bankuna Da Su Fara Biyan Sabbin Kudi a Kanta Hoto: @cenbank
Asali: Twitter

Ya kuma ce wannan matakin an dauke shi ne domin rage cunkoson da ake sabu a wuraren ATM a fadin kasar.

Sabbin kudi za su kai hannun kowa, CBN

A cikin jawabin nasa, Emefiele ya ba yan Najeriya tabbacin cewa za su samu karbar sabbin kudin a kan kanta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yan Najeriya na ta kokawa game da karancin sabbin kudade a kasar amma babban bankin ya bayyana cewa yana aiki da masu ruwa da tsaki don dakile kalubalen, rahoton The Guardian.

CBN ya ce:

"CBN na kokarin tabbatar da ganin cewa sabbin kudin sun kai hannun daukacin yan Najeriya nan ba da jimawa ba.
"Tare da hadin gwiwar hukumar EFCC da ICPC, CBN na ta gudanar da binciken ganin da ido a akwatunan ATM din bankuna."

Haramun ne liki, takawa da siyar kudi

Kara karanta wannan

Samun wuri: Matar da ta gawurta wajen siyar da Nara ta kare a hannun ICPC, an gano masu bata kudi

Har ila yau, gwamnan na CBN ya nuna damuwarsa kan yadda wasu mutane ke siyar da kudaden kasar yana mai jadadda cewar wadannan mutane ba masu kishin kasa bane, domin a cewarsa siyar da kudi, lika shi ko buga tambari a kansa ya saba doka, rahoton Vanguard.

Ya ci gaba da cewa:

"Don kore shakku, sashi na 21(3) na dokar babban bankin Najeriya na 2007 (kamar yadda aka gyara) ya bayyana cewa liki, rawa ko taka kudin da banki yasamar yayin wani taron jama'a za a dauke shi a matsayin cin mutunci da wulakanta takardar naira kuma hukuncinsa a doka shine cin tara ko zaman gidan yari ko kuma dukka biyun."

Legit.ng ta tuntubi wasu yan Najeriya don jin halin da suke ciki a wannan yanayi da ake.

Mallam Ahmad Isma’il ya ce:

“Gaskiya babu abun da za mu ce sai Innalillahi wa’inna Illaihi raji’un. Amma tabbass ana cikin yanayi. Da safen nan haka na tashi babu ko sisi haka na karade unguwarmu babu kudi, a POS din da na zo na samu kuwa wai idan zan ciri N10,000 sai na ba da N1,000 la’ada.

Kara karanta wannan

Kada ku sake kara wa'adin daina amfani da Naira, Atiku ga CBN

“Wannan wacce iriyar rayuwa ce. Idan har akwai laifin gwamnati toh muma mutane akwai namu a ciki. Bama so wa kanmu sauki da zaran an ce akwai dan matsala sai kowa ya daura buri ya ce sai ya amfana daga wannan annobar. Allah ya sawwake.

Mallam Abubakar kuwa cewa ya yi:

“Muna fatan wannan sabon tsari na CBN ya zamo mana alkhairi. Idan har bankuna za su yi yadda aka ce ina kyautata zaton za a samu raguwar matsin da ake ciki a yanzu.”

Bankuna za su ci gaba da karban tsoffin kudi bayan cikar wa'adin CBN, Emefiele

A baya mun ji cewa Godwin Emefiele ya bayyana cewa ko bayan cikar lokacin da CBN ya diba na daina amfani da tsoffin kudi a kasar, bankuna za su ci gaba da karbarsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel