Magidanci ya Kona Matarsa Saboda ta ki yin Abinci, Tayi Masa Wankin Tufafinsa

Magidanci ya Kona Matarsa Saboda ta ki yin Abinci, Tayi Masa Wankin Tufafinsa

  • Rundunar 'yan sandan Ogun ta sanar da kama wani Hassan Azeez kan zargin watsawa matarsa fetur tare da cinna mata wuta
  • Ya sanar da 'yan sanda cewa ta ki yi masa abinci ne duk da bakar yunwar da ya ke ji amma ta kare da wanke tufafinsa
  • Ya aikata laifin tun watan Oktoba amma sai Janairu 'yan sanda suka kama shi, ya alakanta lamarin da aikin zugar shaidan

Ogun - Rundunar 'yan sandan jihar Ogun sun damke wani Hassan Azeez kan zarginsa da ake yi da bankawa matarsa wuta.

Taswirar Ogun
Magidanci ya Kona Matarsa Saboda ta ki yin Abinci, Tayi Masa Wankin Tufafinsa. Hoto daga Thecable.ng
Asali: UGC

Abimbola Oyeyemi, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Ogun, a wata takardar da ya fitar ranar Juma'a, yace mahaifin wacce abun ya ritsa da ita ne ya kai karar a ranar 22 ga Oktoban 2022.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Sufeta Janar Na Yan Sandan Najeriya Ya Umurci A Kama Masu Sayar Da Takardun Naira

Oyeyemi yace wanda ake zargin ya tsere bayan an aika 'yan sanda su kama sa a inda lamarin ya faru.

Kakakin rundunar 'yan sandan yace an kama Azeez a ranar 22 ga watan Janairun 2022, jaridar The Cable ta rahoto.

A yayin bayanin abinda ya faru ga 'yan sanda, wanda ake zargin yace matarsa mahaifiyar yaro daya, ta ki yi masa abinci saboda wankin kayan da ta ke yi.

"Bayan tuhumar wanda ake zargin, yace ya tsere zuwa Jamhuriya Benin amma ya sanar da haukumar cewa aikin shaidan ne."

- Kakakin rundunar 'yan sandan Ogun ya sanar.

“Kamar yadda yace, ya bukaci wacce abun ya ritsa da ita da tayi masa abinci amma maimakon hakan sai ta mayar da hankali kan wanke kaya.
“Ya bayyana cewa lamarin ya fusata shi saboda ya na matukar jin yunwa kuma fushin ne yasa ya watsa mata fetur tare da banka mata wuta.

Kara karanta wannan

Shahararren Sarki Ya Ragargaji Emefiele, Ya Ce Ƙarancin Takardun Naira Barazana Ne Ga Rayuwan Yan Najeriya

"A yayin da aka tambaye shi kayan waye ta ke wankewa, yace kayan shi ne ta ke wankewa."

- Ya tabbatar.

Gwamnonin APC sun roki Buhari da ya bari ana amfani da tsoffi da sabbin Naira

A wani labari na daban, Gwamnonin APc da suka gana da Shugaba Buhari sun roke shi da ya bari 'yan Najeriya su cigaba da amfani da dukkan takardun kudin, sabbi da tsofaffi.

Gwamna El-Rufai na jihar Kaduna yace CBN tayi nasara kwashe N2 tiriliyan amma N300 biliyan kadai ta buga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng