Sufeta Janar Na Yan Sandan Najeriya Ya Umurci A Kama Masu Sayar Da Takardun Naira

Sufeta Janar Na Yan Sandan Najeriya Ya Umurci A Kama Masu Sayar Da Takardun Naira

  • Rundunar yan sanda ta dauki matakin taka wa wasu da ke sayarwa yan Najeriya takardun naira birki
  • Usman Alkali Baba, sufeta janar na yan sandan Najeriya ya bada umurnin a kama tare da hukunta duk wani da aka kama yana sayar da sabbin nairorin
  • Wasu mutane sun fara sayar da takardun nairan ne saboda karancin kudin da aka samu a cikin yan kwanakin nan

FCT, Abuja - Usman Alkali Baba, sufeta janar na rundunar yan sandan Najeriya, IGP, ya bada umurnin a kama tare da hukunta mutane da ke sayar da naira da cin mutuncinta, rahoton The Cable.

IGP din a ranar Juma'a ya umurci mataimakin sufeta janar na yan sanda mai kula da sashin bincike na FCID da mataimakin sufeta janar na tattara bayanan sirri, FIB, su kasance 'cikin shiri'.

Kara karanta wannan

Jan aiki: Daga lika sabbin Naira a gidan biki, EFCC ta kama wata fitacciyar 'yar fim

Alkali Baba
Sufeta Janar Na Yan Sandan Najeriya Ya Umurci A Kama Masu Sayar Da Takardun Naira. Hoto: @daily_trust
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce a hukunta dukkan wadanda aka kama suna sayar da takardun naira da babban bankin Najeriya ta fitar ko cin zarafin kudin kamar yadda dokar babban bankin kasa na 2007 ya tanada.

Yan Najeriya da dama na shan wahala wurin samun sabbin takardun nairan a yan kwanakin nan, saboda karancinsu a bankuna da na'urar ATM.

Hakan ya sa wasu mutane ke amfani da wannan damar suna cin kazamar riba, suna sayar da kudi ga al'umma a kan farashi mai tsada.

Za a hukunta duk wanda aka kama yana sayar da takardun naira, IGP na yan sandan Najeriya

Kakakin rundunar yan sandan Najeriya, CSP Muyiwa Adejobi, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Juma'a ya ce Baba ya umurci mataimakin sufeta su kama tare da hukunta dukkan wadanda aka samu suna sayar da sabbin nairorin da CBN ke fitarwa.

Kara karanta wannan

Magidanci ya Watsawa Matarsa Fetur Tare da Cinna Mata Wuta Saboda ta ki Masa Girki a Ogun

Ya ce IGP din kuma ya bukaci dukkan mataimakin sufeta janar da kwamishionin yan sanda da ke kula da yankunansu su aiwatar da tanade-tanaden sashi na 20 da 21 na dokar babban bankin Najeriya ta 2007, rahoton Daily Trust.

Dokar ta haramta 'tallata ko sayar da takardun naira da yin liki ko rawa da taka takardun naira, buga jabunsu da rashin karbar naira a matsayin kudi ko lalata kwandala ko takardan kudin da CBN ta fitar.'

Ya kara da cewa:

"Sufeta janar na yan sandan ya jadada cewa rundunar yan sandan Najeriya ba za ta yi kasa a gwiwa ba wurin aiwatar da dokokin kasa ta kuma yi kira ga sauran hukumomin tsaro su hada kai tare da rundunar yan sandan don hukunta wadanda ke saba dokar CBN, da sauran dokoki a Najeriya."

Babban Bankin Najeriya Ya Tsawaita Wa'adin Amfani Da Tsaffin Takardun Naira, Ya Bada Sabon Wa'adi

Kara karanta wannan

Karancin Naira: Fusatattun Matasa Yan Zanga-Zanga Sun Kai Hari Ofishin Gwamna

Bayan korafe-korafe, babban bankin Najeriya, CBN, ya tsawaita wa'adin cigaba da amfani da tsaffin takardun naira a Najeriya.

Godwin Emefiele, gwamnan na CBN ne ya sanar da hakan cikin wata takarda da ya saka hannu kai a safiyar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel