Dakarun Sojoji Sun Kama Masu Kaiwa Mayakan ISWAP Kayayyaki 13 a Borno

Dakarun Sojoji Sun Kama Masu Kaiwa Mayakan ISWAP Kayayyaki 13 a Borno

  • Dakarun rundunar sojojin Najeriya sun cafke wasu masu kaiwa mayakan ISWAP kayan abinci da sutturu a jihar Borno
  • Dubbun yan aiken mayakan kungiyar ta'addancin su 13 ya cika a lokacin da dakarun Operation Hadin kai da yan CJTF suka yi sintiri a kasuwar Benishiek
  • Kamar yadda majiya ta bayyana, masu zuwa wa yan ta'addan aike kan shiga kasuwa duk ranar da kasuwanni ke ci don siya masu kayan abinci, fetur da sauransu

Borno - Dakarun rundunar sojoji na Operation Hadin Kai da ke yaki da ta'addanci a yankin arewa maso gabas sun kama masu kaiwa mayakan ISWAP kayayyaki su 13 a jihar Borno.

An tattaro cewa dakarun Brigadiya ta 29 da ke Benishiek, tare da hadin gwiwar yan sa-kai na CJTF sun kama wadanda ake zargin yayin wani binciken kasuwa da suka yi a kasuwar Benishiek.

Kara karanta wannan

Yan ISWAP Sun Koma Fashi, Sun Kutsa Wani Gari A Biu Don Satar Magunguna A Borno

Jihar Borno
Dakarun Sojoji Sun Kama Masu Kaiwa Mayakan ISWAP Kayayyaki 13 a Borno Hoto: TheCable
Asali: UGC

Wasu majiyoyin tsaro sun sanar da Zagazola Makama, kwararren masanin lamuran tsaro a tafkin Chadi cewa an kama wadanda ake zargin ne dauke da kayayyaki masu yawa da za su kaiwa mayakan ISWAP.

Majiyoyin sun bayyana cewa garuruwan Benisheikh da Jakana a karamar hukumar Kaga na daya daga cikin manyan wuraren da ke samar da kayan amfani ga mayakan Boko Haram da ISWAP na tsawon shekaru masu yawa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce a ranar kowace kasuwa, yan aiken yan ta'addan kan shiga kasuwa don siyawa miyagun kayan abinci iri-iri, man fetur, layukan waya, tufafi da sauran kayayyaki.

Zagazola Makama ya kuma rahoto majiyar na cewa dakarun sun sha kama bara-gurbin da ke yiwa yan ta'addan aiki.

Sojoji sun murkushe kwamandan Boko Haram da mayaka 32 a jihar Borno

A wani labarin kuma, dakarun rundunar Operation hadi kai tare da taimakon yan CJTF sun murkushe mayakan kungiyar ta'addanci na Boko Haram 32 a jihar Borno.

Kara karanta wannan

Wa’adin CBN: Mutanen Karkara Sun Koma Cinikin Bani Gishiri Na Baka Manda Yayin da Sauya Kudi Ke Huta Wutan Yunwa a Gari

Sojojin sun farmaki mabuyar yan ta'addan inda suka yi zazzafar musayar wuta amma daga karshe suka ci galaba a kan mayakan tare da yi masu mummunan illa.

A yayin artabun, sojojin sun kuma yi nasarar kawar da sbabban kwamandan Boko Haram mai suna Abu Illiya a sansaninsu da ke karamar hukumar Konduga ta jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng