Yan ISWAP Sun Koma Fashi, Sun Kutsa Wani Gari A Biu Don Satar Magunguna A Borno

Yan ISWAP Sun Koma Fashi, Sun Kutsa Wani Gari A Biu Don Satar Magunguna A Borno

  • Wasu da ake kyautata zaton yan ta'addan kungiyar slamic State of the West African Province (ISWAP) sun kai hari a garin Gur, Jihar Borno
  • Maharan da aka rahoto cewa sun kutsa garin a kan babura sun rika harbe-harbe da bindiga sannan suka sace magunguna daga cibiyoyin lafiya
  • Rahotanni da aka ce an samu daga sahihan majiyoyi sun bayyana cewa yan ta'addan sun cika wandunansu da iska yayin da suka hango sojoji suna isowa

Jihar Borno - Wasu da ake zargin mayakan kungiyar ta'addanci na Islamic State of the West African Province (ISWAP) sun kai hari garin Gur da ke karamar hukumar Biu a jihar Borno, Zagazola ya rahoto.

Wasu sahihan majiyoyi sun fada wa Zagazola Makama, kwararre a bangaren nazarin yaki da ta'addanci da tsaro a tafkin Chadi, cewa yayin harin da aka kai a ranar 29 ga watan Janairu, yan ta'addan sun kona cibiyar lafiya ta bai daya sun kuma sace magunguna.

Kara karanta wannan

Borno: ISWAP Sun Yi Rabon Tsofaffin Kudi ga Fasinjojin Motocin Haya Kyauta, Sun ce SU je Bankuna Su Canza su

Taswirar jihar Borno
ISWAP Sun Koma Fashi, Sun Kutsa Wani Gari A Biu Don Satar Magunguna A Borno. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

Yan ISWAP sun sace magunguna a cibiyar lafiya a Gur

Yan ta'addan sun kai hari cibiyoyin lafiya domin su sace magunguna da za su kula da mayakansu da suka jikkata yayin aramgama da sojoji a Damboa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Majiyoyin sun ce yan ta'addan sun kutsa garin a kan babura, kuma suka fara harbe-harbe hakan ya tilastawa mutane tserewa.

Ya ce yan ta'addan sun tsere bayan sun hango jami'an tsaro na bataliya ta 231 na Operation Hadin Kai.

A cewarsa, ya ce babu wanda ya rasa ransa sakamakon harin da yan ta'addan na ISWAP suka kai.

Yan Ta'adda Masu Yawa Sun Mutu Yayin Da ISWAP Da Boko Haram Suka Yi Bata Kashi Na Awa 14

A baya mun kawo muku rahoton cewa majiyoyi masu masaniya kan kungiyar Boko Haram ta ce yan kungiyar da dama sun mutu sakamakon wata arangama da suka yi da ISWAP.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Kanawa Sun Yi Bore, Rikici Ya Barke a Jihar Kano Bayan Ziyarar Buhari

A cewar majiyar, wasu mayaka da dama karkashin jagorancin Abu Umaimah da wasu kwamandojin guda hudu ne suka kutsa sansanin ISWAP a Tumbum Allura dake karamar hukumar Kangar, arewa maso gabashin garin Abadam da ke jihar Borno.

Zagola ya rahoto cewa majiyoyi masu tattara bayanai na sirri sun ce an fara arangamar tsakanin kungiyoyin biyu ne tun misalin karfe 4 na yammacin ranar Juma'a har zuwa karfe 5 na asubahin ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel