Tsohuwar Ministar PDP Tayi Shiri, Ana Kokarin Dawo da Dukiyoyinta da Aka Karbe

Tsohuwar Ministar PDP Tayi Shiri, Ana Kokarin Dawo da Dukiyoyinta da Aka Karbe

  • Diezani Alison-Madueke ba ta gamsu da raba ta da wasu dukiyoyinta da Alkalin kotu ya yi ba
  • Tsohuwar Ministar Najeriyar ta shigar da kara a kotun tarayya a Abuja, tana kalubalantar matakin
  • Lauyan da ya tsayawa Alison-Madueke ya zargi kotu da kuskure da yanke hukunci ba da adalci ba

Abuja - Tsohuwar Ministar harkokin man fetur, Diezani Alison-Madueke ta gabatar da roko gaban babban kotun tarayya da ke zama agarin Abuja.

Rahoton Punch ya bayyana cewa Misis Diezani Alison-Madueke ta na so kotun tarayyar ta janye umarnin da aka bada na karbe wasu kadarorinta.

Hukumar EFCC tayi nasarar raba tsohuwar Ministar da wasu kaya da ta mallaka, hakan ta sa ta nemi alfarmar kotu domin a dawo mata da kayan.

Hukumar dillacin labarai na kasa ta ce Alison-Madueke ta shigar da wannan kara ne a lokacin da EFCC ta ke kokarin yin gwanjon kayayakin na ta.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Yanke Hukunci a Shari’ar Yunkurin Tsige Buhari daga Mulki a Kan Zaben 2019

Tsohuwar Minista
Diezani Alison Madueke Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An dauko hayar Mike Ozekhome SAN

Babban lauyan nan, Mike Ozekhome, SAN shi ne wanda ya tsayawa tsohuwar Ministar tarayyar a karar da ta ke gaban Mai shari’a Inyang Ekwo.

Jaridar ta ce hukumar EFCC ce kadai wanda Ozekhome, SAN yake tuhuma a kotun Abujan.

Inda aka yi kuskure Inji Mike Ozekhome SAN

Lauyan da ya tsayawa Alison-Madueke yana ikirarin ba ayi mata adalci an saurare ta a lokacin da ake shari’ar ba, sai kurum aka ba EFCC gaskiya.

Mike Ozekhome wanda ya yi fice a harkar shari’a, ya fadawa Inyang Ekwo cewa kotu ta rika zartar da hukunci a kan lamarin da ba ta da hurumi a kai.

Lauyan ya kara da cewa, an sabawa sashe 36 (1) na kundin tsarin mulkin Najeriya a yunkurin ba EFCC damar yin gwanjon kayan tsohuwar Ministar.

Kara karanta wannan

Duk da Barazanar Tsaro, Shugaba Buhari Ya Dura Kano, Zai Kaddamar da Jerin Ayyuka

Vanguard ta rahoto ‘yar siyasar ta na cewa ba ta taba ganin takardun tuhumar da ake yi mata ba, haka zalika ta ce ba ta san da hujjojin da ke kanta ba.

A cikin korafin da ta gabatar a wannan karo, Alison-Madukwe ta ce an yaudari kotu ne wajen karbe mata dukiyar da ta mallaka ba tare da hujjoji ba.

Nasara tana waje Tinubu -Gwamna

A wajen yawon kamfe, an samu labari Gwamna Rotimi Akeredolu ya fadawa mutanen Ondo Bola Tinubu zai lashe zaben shugaban kasa da za ayi.

Shugaban Jam’iyyar APC a Ondo, Ade Adetimehin ya jagoranci taron yakin neman zaben da aka shirya inda Gwamnan ya rabawa ‘yan takaransu tutoci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel