Kotu Ta Yanke Hukunci a Shari’ar Yunkurin Tsige Buhari daga Mulki a Kan Zaben 2019

Kotu Ta Yanke Hukunci a Shari’ar Yunkurin Tsige Buhari daga Mulki a Kan Zaben 2019

  • Ambrose Owuru ya gagara samun nasara a kan karar da ya shigar a kan Muhammadu Buhari da INEC
  • Buhari ya doke ‘Dan takaran Jam’iyyar Hope Democratic Party a zaben 2019 a kotun tarayya da ke Abuja
  • Cif Owuru yana so Hukumar INEC ta tsaida shi a matsayin asalin wanda ya yi nasara a zaben da ya gabata

Abuja - Babban kotun tarayya mai zama a garin Abuja ta saurari karar da Ambrose Owuru a kan Mai girma shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

Punch ta rahoto cewa an yi watsi da karar Ambrose Owuru wanda ya yi takarar kujerar shugabancin kasar nan a karkashin HDP a zaben 2019.

Alkali Inyang Ekwo ya saurari korafin da Lauyan Ambrose Owuru ya shigar a gabansa.

Wadanda aka yi kara a shari’ar su ne Muhammadu Buhari da ya tsayawa APC takara a zaben da ya wuce da kuma hukumar gudanar da zabe a Najeriya.

Kara karanta wannan

Duk da Barazanar Tsaro, Shugaba Buhari Ya Dura Kano, Zai Kaddamar da Jerin Ayyuka

Hukuncin Inyang Ekwo

Daga cikin abin da Alkalin ya dogara da shi; Lauyan tsohon ‘dan takaran ya sabawa dokoki, ya yi wa kotun koli karan tsaye da karar da ya shigar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An rahoto Inyang Ekwo yana cewa karar da Cif Ambrose Owuru ya kai gabansa, bai da tushe ko makama, saboda haka babu bukatar a saurare shi.

Buhari
Shugaba Buhari a taron APC Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Korafin Ambrose Owuru

Owuru wanda Lauya ne da ya yi karatu a Birtaniya, ya yi karar Buhari da hukumar INEC, yana so a ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben 2019.

Lauyan ya kuma kalubalanci hukumar INEC a dalilin dage zaben shugabancin kasa da tayi a 2019 daga ranar 16 ga Fubrairu zuwa 23 ga watan Maris.

Daily Post ta ce Alkalin da ya saurari shari’ar da aka shigar a kan INEC da ‘dan takaran APC a zaben da ya wuce, ya ki amincewa da rokon mai kara.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamnan APC Ya Maka ‘Dan Jam'iyyarsa a Kotu, Ya Ce Dole Ya Biya Shi N250m

A daidai lokacin da aka zartar da wannan hukunci a game da abin da ya faru a zaben 2019, watanni kusan uku suka ragewa Muhammadu Buhari a ofis.

Shugaba Buhari a Kano

Dazu aka ji labari Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari bai karaya a kan rade-radin barazanar tsaro ba, ganin abin da ya faru da shi a jiharsa ta Katsina.

Tawagar Buhari ta isa Kano domin kaddamar da ayyuka a safiyar yau. Jama’a na ta tofa albarkacin bakinsu game da wannan ziyara da aka yi tunanin za a fasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel