Yadda Waya Nokia 3310 Ta Shekara 20 a Ajiye, Aka Kunna Aka Ganta da Caji 70% Ya Girgiza Intanet

Yadda Waya Nokia 3310 Ta Shekara 20 a Ajiye, Aka Kunna Aka Ganta da Caji 70% Ya Girgiza Intanet

  • Waya Nokia 3310 da aka ajiye na tsawon shekaru 20 ta ba da mamaki bayan ganinta da caji kaso 70% bayan tsawon lokaci
  • Kevin Moore ta bayyana cewa, ta gano wayar ne a ciki dankin ajiye kaya a lokacin da take neman makullan da ta adana
  • A wannan zamanin, tsanani batirin waya ya kai kwanaki uku ne, daga nan dole a yi caji ko kuma a zauna babu amfani

Abu na karshe mai ban mamaki da Kevin Moore, wata ‘yar kasar Amurka ta gani a dankin ajiye kayanta shine wata tsohuwar waya kirar Nokia 3310.

Amma babban abin da ya bata mamaki ba wai wayar bace kawai, Moore ta firgita lokacin da ta ga wayar da caji 70%.

Nokia 3310 ta ba da mamakin da ba a taba gani ba
Yadda Waya Nokia 3310 Ta Shekara 20 a Ajiye, Aka Kunna Aka Ganta da Caji 70% Ya Girgiza Intanet | Hoto: :Oliver Helbig
Asali: Getty Images

Ta kunna wayar bayan shekaru 20

Moore ta shiga mamaki lokacin da take kakkabe komai na cikin dankin domin nemo makullai sadda ta gamu da wayar Nokia kirar 3310.

Kara karanta wannan

Amarya Ta Antayawa Uwarginta Tafasashen Ruwa Kan Zargin Maita A Jihar Kwara

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ta ga wayar sannan ta kunna, kuma abin mamaki, duk da shekaru 20 ba a taba wayar ba, har yanzu da cajinta 70%.

Moore ta ce, ba za ta iya tuna yaushe ne ta saka wayar a caji ba, kai karshe ma bata cajar waya Nokia.

A wannan zamanin, wayoyon iPhone da Android ba su cika wuce kwanaki uku da caji ba, sukan bukaci caji a kullum domin a iya aiki dasu.

Martanin jama’a

Nokia dai har yanzu na kera wayoyin hannu masu kyau, amma kamfanin ba ya yin wayoyi masu rike caji kamar 3310 da aka yi yayi a shekarun baya.

Wani da ya rubuta cewa:

“Batirin Nokia 3310 kamar wani zubi ne na har abada. Bai kamata ace akwai shi ba, amma akwai. Nokia 3310 guda daya za ta iya ba gari guda makamashi."

Kara karanta wannan

Bidiyon Dirarriyar Amarya Mai Shekaru 57 da ke Nuna Yarinta, Ta Saka Jar Riga ta Amaren Zamani

A cewar rahotanni, an daina ganin Nokia 3310 saboda barazanar wata boyayya game da amfani da man da aka hako a kasa, cewa batirin wayar zai iya lalata fannin masana’antar samar da man fetur daga kasa.

Babu batirin wayan da ke kai wannan dadewa, inji wasu mutanen

A bangare guda, wasu mutane sun musanta labarin tare da cewa, ba za a taba samun batirin waya da zai yi wannan dadewa da caji ba ba tare da an saka shi caji ba.

Rahoton ya ce:

“Babu wani batirin da za a siyarwa mutane da zai kai shekaru 20 ba tare da an yi masa caji ba.”

A gaba kuma, wata kafar labaran barkwanci da shagube ta Chesterbungle ta buga labarin a kafarta.

Kafar dai ta yi shura ne wajen yin maudu’ai masu ban dariya da ke nesanta kai ga gaskiyar gundarin labari, don haka ake tunanin labarin batirin Nokia 3310 din ma na kanzon kurege ne.

Kara karanta wannan

Ba Zamu Karba Kudin da Zasu Zama Takardun Tsire ba: 'Yan Bindiga Sun ki Karbar Tsofaffin N5.3m na Fansa a Kaduna

Wani rahotonmu a baya ya bayyana yadda za ku ke sanya caji lafiya, da kuma kaucewa kura-kurai da ke tattare da rashin kula wajen sa batir a caji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel