Mata Mai Shekaru 57 Ta Amarce, Ta Cakare da Kayan Amaren Zamani a Bidiyo

Mata Mai Shekaru 57 Ta Amarce, Ta Cakare da Kayan Amaren Zamani a Bidiyo

  • Wata kyakkyawar mata 'yar shekara 57, da ta auri masoyinta tana sanye da hadaddiyar jar riga ta yi yawo a dandalin soshiyal midiya
  • Mahaifinta mai shekaru 80 ne ya rakota wajen shagalin bikin, wanda kamanninsa ke nuna kasa da shekarunsa
  • Bidiyon shagalin bikin da aka wallafa a kafar TikTok, ta dauki hankalin masoya ado da dama, wanda a yanzu sama da 1.2 miliyan mutane suka yi arba da bidiyon

Wata kyakkyawar mata mai shekaru 57 ta amarce da masoyinta, sanye da doguwar rigar da ta zauna mata a jiki rana aurenta.

Amarya
Mata Mai Shekaru 57 Ta Amarce, Ta Cakare da Kayan Amaren Zamani a Bidiyo. Hoto daga TikTok/@blondlocs
Asali: UGC

Matar ta wallafa guntun bidiyon lokacin da ta isa wajen bikin. A halin yanzu, sama mutane 1.2 miliyan ne suka yi arba da bidiyon.

Mahaifinta mai shekaru 80 ne ya rakota da angon. Mutumin kwata-kwata bai yi kama da shekarunsa ba saboda yadda tsufa bai nuna ko kadan a tattare da shi ba.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Ana Tsaka da Shagalin Aure, Takardar da Wani ya Mikawa Amarya ta Tada Hankalin Ango

Alamu sun nuna amaryar ta gaji kyawun siffarta ne daga mahaifinta saboda, a shekaru 57, wasu masoya a TikTok sun kasa yarda ta kai shekarun.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ita da mahaifin nata suna taku kamar sojoji zuwa wajen bikin cike da farinciki da kwanciyar hankali. Wadanda suka kalli bidiyon sun yi mamakin yadda mijin zai yi idan ya ganta.

Ta amsa da cewa ya fashe da kuka ne. Saboda yadda ta kauracewa farar rigar da amarya ta saba sanya wa ranar bikinta, inda ta yi amfani da ja wanda ta kayartar da mutane da dama.

@blondlocs ce ta wallafa bidiyon a dandalin TikTok.

Martanin 'yan soshiyal midiya

@Sadeara White647 ta ce:

"Idan angonki ya hango kina taho wa gare shi zai bukaci na'urar taimakon numfashi saboda zaki tafi da gaba daya da numfashinsa."

Kara karanta wannan

Bidiyo: Budurwa Baturiya ta Bayyana Yadda 'Dan Yahoo Ya Karbe Kudin Mahaifiyarta da Soyayya

@Buffie Hipps ta yi tsokaci:

"Ina rokonki da ki nuna mahaifinki, mijina bai yarda mahaifinki ya kai 80 ba. Ina rokonki fada mana gaskiya."

@user7603115902413 ta ce:

"Kin yi matukar kyau!"

@Felicia Morton210 ta yi martani:

"Kin yi kyau. Da kika tsaya nasha mahaifinki shi ne angonki. Ku biyun ba ku yi kama da shekarunku ba. Ina taya ku murna."

@13_Bella_30 ta ce:

"Kai, ku biyun kun yi matukar kyau. Kuna daukar ido kuma mahaifinki ya kai 80, ba zai yiwu ba."

Ana tsaka da shagalin aure, an tadawa ango hankali

A wani labari na daban, ana cikin shagalin aure wani ya mikawa amarya takarda wacce ta tayarwa ango hankali.

Tuni matashin ya dinga lekawa don ya gane me aka rubuto mata, bayan ya karanta ne hankali ya kwanta inda ya ga fatan alheri aka yi musu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel