Manyan kura-kurai 5 da mutane ke tafka wa yayin cajin waya

Manyan kura-kurai 5 da mutane ke tafka wa yayin cajin waya

Wayoyin hannu, da aka fi kira da da 'Salula', sun zama wani ginshikin bangare na rayuwar mutane. Mutum kan shiga damuwa duk lokacin da wayarsa ta hannu ta samu wata matsala ko kuma ta lalace gaba daya.

Legit.ng ta kawo muku wasu hanyoyi da zaku inganta lafiyat batirin wayoyinku na hannu ta hanyar kiyaye wasu manyan kura-kurai da jama'a ke tafka wa yayin cajin wayar hannu.

1. Barin waya sai ta batiri yayi karkaf kafin a saka caji: Masana fasaha da ilimin kimiyyar wayar hannu sun bayyana cewa barin waya sai caji ya kare karkaf kafin a sake yin wni cajin yana haddasa saurin gajiyar batiri, wanda daga bisani ma sai karfin batirin waya ya yi kasa, ya kasance ba ya rike caji kamar yadda kamar yadda ya kamata.

Masana sun bayar da misali da jikin mutum da abinci. Kamar yadda mutum ke cin abinci tun kafin yunwa ta kashe shi, haka ya kamata yake yi wa batirin waya caji kafin ta mutu.

2. Barin waya ta kwana tana caji: Da yawan mutane kan saka wayarsu caji kafin su kwanta. Hikimarsu ta yin hakan shine su tashi su ga wayarsu ta cika da caji.

Masana sun bayyana cewa batirin waya na cika da caji ne cikin sa'a biyu ko kasa da haka, sannan mutum kan yi barci na a kalla sa'a biyar zuwa takwas, lokacin da suka ce yayi yawa a bar waya tana caji. A cewar masana fasahar waya, barin batirin waya yana gasuwa a kan wutar lantarki bayan waya ta cika yana saurin gajiyar da batiri da ma haifar da mutuwar sa.

3. Barin waya a cikin riga (Case) yayin caji: Wayar hannu kan fitar da wani huci duk lokacin da ake cajin batiri. Masana sun bayyana cewa barin wayar hannu a cikin rigar ta yayin caji kan hana hucin da wayar ke huro wa ya fita daga cikinta, lamarin da yasa waya kan dauki zafi yayin da ake yi mata caji. Daukan zafin da waya ke yi kan iya kashe batirin ta gaba daya.

DUBA WANNAN: Da duminsa: Shugaba Buhari ya tashi zuwa kasar Japan (Hotuna)

4. Cajin waya a wurin da bai dace ba: Wayoyin hannu na da iyaka ta fuskar zafi ko sanyin da suke bukata da kuma adadin wutar da suke so domin yin caji yadda ya kamata.

Masana sun shawarci masu wayar hannu su kula da wurin da zasu saka cajin wayoyinsu da kuma karfin wutar da zasu yi amfani da shi domin cajin wayarsu. Yin cajin waya a wuri mai tsananin zafi ko sanyi ko a wutar lantarki da karfinta ya yi yawa ko kuma ya yi kadan kan haddasa mutuwar batirin waya ko kuma ya rage masa kuzari.

5. Cajin waya da kowacce irin caja da mutum ya samu: Kusan dukkan manyan wayoyin hannu kirar fasahar 'Android' na amfani da samfurin caja mai kan USB, lamarin da yasa mutane ke yin amfani da duk cajar da suka samu matukar zata shiga gurbin cajin wayarsu. Duk da kasancewar kusan kan cajin wayar 'Android' iri daya ne a ido, an tsara kowacce waya domin ta yi amfani da samfurin kan caja da yafi dacewa da kirar wayar. A saboda haka, yin amfani da kowanne kan caja da mutum ya samu kan iya bayar da gagarumar gudunmawa wajen saurin lalacewar batirinsa ko ma wayarsa baki daya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel