Fashewar Bam Ya Raba Mutum 8,000 Da Muhallansu A Shararriyar Jihar Arewa

Fashewar Bam Ya Raba Mutum 8,000 Da Muhallansu A Shararriyar Jihar Arewa

  • Sama da mutum 8,000 ne suka bar gidajen su sakamakon fashewar bam a Karamar hukumar Shiroro
  • Wani jirgin yaki mallakar sojojin Najeriya ne yayi kuskuren jefa bam bisa kuskure kan jami'an sintiri
  • Wanda abin ya shafa sun bayyana cewa tun suka zo sansanin yan gudun hijira ba wani jami'in gwamnati da ya kawo musu dauki

Akalla mutane 8,150 ne suka rasa mahallansu daga yankin Galadima-Kogo da kewaye a Karamar hukumar Shiroro ta Jihar Niger bayan da wani jirgin yaki ya tarwatsa yankunan da bam ranar 24 ga watan Janairu.

An kashe jami'an sintiri da dama, yayin da manyan kwamandojin suka ji mugwayen raunuka, rahoton Daily Trust.

Taswirar Jihar Neja
Fashewar Bam Ya Raba Mutum 8,000 Da Muhallansu A Shararriyar Jihar Arewa. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Canjin Takardun Kudi: Kira Zuwa Ga Hukuma, Daga Dr Sani Rijiyar Lemo

An samu yan gudun hijira da dama ta aka killace a sansanonin yan gudun hijira.

Sakataren gwamnatin Jihar Niger, Alhaji Ahmed Matane, ya bayyana cewa jirgin mallakar hukumar sojin sama ta kasa ne kuma jami'an basu san akwai jami'an tsaro a yankin ba.

Ya kuma bayyana cewa gwamnati na sane da yan gudun hijirar da ke killace a yankin.

Matane yace gwamnati ta tattauna shugabannin Karamar hukumar Shiroro da kuma hukumar North-South (NSP) don samawa yan gudun hijirar muhalli da kuma walwala.

''Muna yin bincike don magance matsalar muna kuma bibiyar batun wanda suka rasa rayukan daga hannun jami'an tsaro wanda tsautsayi ya afka musu.
''Mun samu mace-mace kuma muna kula da wanda suka ji ciwo a asibiti.
''Kayayyakin taimakon gaggawa sun isa ga majinyata kuma muna tabbatar da cewa akwai cikakken tsaro a sansanin yan gudun hijira,'' a cewarsa.

Daya daga cikin wanda suka rasa muhallansu, Hajiya Rabi Musa, ta shaidawa kamfanin dillacin labarai na kasa (NAN) cewa mazauna yankin sun ga jiragen suna wucewa kafin daga bisani suji wata mummunar kara da ta girgiza yankin.

Kara karanta wannan

Babu wanda ya yiwa Buhari Ihu ko Rajamu a Katsina, amma mun kama masu tada tarzoma 8: Yan Sanda

''An kashe mana mutane da yawa, bayan jami'an sintiri. Mun gudu don neman tsira a wuraren da NSP ta tanada; yanzu ba kowa a garuruwan mu; sun zama kufayi.
''Tun da muka zo nan, ba wanda ya kawo mana tallafi; ba wani jami'in gwamnati ko guda daya. Bamu da ruwan sha, bare kuma zancen wanka; muna shan matukar wahala,'' a cewar matar.

Shugaban matasan Galadima-Kogo, Malam Ibrahim Bahago, ya ce an shaidawa mutanen yankin a ranar Talata cewa yan bindiga suna yawo anan yankin.

Ya ce jami'an sintiri sun shiga zagaye a titin da yan bindigar suke bi hade da sauran jami'an tsaro kafin a musu ruwan harsashi.

''An yi wa yan sintitinmu ruwan harsashi kafin daga bisani muji kara mai karfi ashe bam aka jefawa yan sintirin da suke kula damu. Da yawansu sun mutu.
''Tunda muka zo nan ba wani jami'in gwamnati da ya kawo mana dauki."

Bahago ya zargi gwamnatin jihar da wofantar da yan gudun hijirar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164