Hawaye Yayin Da Dan Majalisar Wakilai Na Tarayya Na PDP Ya Rasu A Abuja

Hawaye Yayin Da Dan Majalisar Wakilai Na Tarayya Na PDP Ya Rasu A Abuja

  • Jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ta shiga zaman makoki a yayin da daya cikin dan takarar ta na babban zaben 2023, Barista Abba Bello Haliru ya rasu
  • Barista Haliru ya rasu ne a Abuja, ranar Juma'a, 6 ga watan Janairu bayan gajeruwar rashin lafiya, a cewar direktan kwamitin kamfen din dan takarar gwamna na PDP, Alhaji Abubakar Shehu
  • Marigayin, dan takarar na jam'iyyar PDP na majalisar wakilai na mazabar Birnin Kebbi/Kalgo/Bunza, shine dan fari ga tsohon shugaban PDP na kasa, Dr Bello Haliru

FCT, Abuja - Dan takarar majalisar wakilai na tarayya na mazabar Birnin Kebbi, Bunza da Kalgo, a karkashin jam'iyyar PDP, Abba Bello Muhammad ya rasu.

Lauyan ya rasu ne bayan gajeruwar rashin lafiya a birnin tarayya Abuja, The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Dan Takarar Gwamnan Ya Takaita Atiku, Jiga-Jigai da Mambobin PDP Sun Koma Bayan Tinubu

Abba Mohammed
Allah Ya Yi Wa Dan Takarar Majalisar Tarayya Na PDP, Bello Muhammad, Rasuwa A Abuja. Hoto: Photo credit: @AbbaBelloMohd
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kwamitin kamfen din gwamna na jam'iyyar, cikin sanarwar da Abubakar Usman ya fitar, a madadin kwamitin watsa labarai, ya yi alhinin rasuwar babban mambansu.

Sanarwar ta ce shugabancin kwamitin kamfen din sunyi bakin ciki tare da kaduwa bisa rasuwar Muhammad.

An dakatar da harkokin kamfen

Kwamitin ta kuma bada umurnin a dakatar da dukkan harkokin kamfen har zuwa wani lokaci nan gaba.

Ciyaman din kwamitin watsa labarai, Alhaji Lawal Gwandu, ta yi kira ga shugabannin PDP da mambobin jihar da magoya baya su yi addu'a Allah ya jikan mammacin.

Kwamitin kamfen din gwamna na jihar ta kuma mika sakon ta'aziyya ga iyalan, masarautar Gwandu da dukkan yan PDP baki daya bisa wannan babban rashin.

Sanarwar ta kara da cewa:

"Allah SWT ya jikansa kuma ya gafarta masa ya saka masa da aljanna firdausi."

Kara karanta wannan

Kogi: Gwamna Ya Aikewa Basarake Tuhuma Kan Kin Fitowa Maraba da Buhari, Ya Zargesa da Raini da Rashin Da'a

Dan Takarar Majalisar Jihar Karkashin PDP a Plateau Ya Rasu

A wani rahoton mai kama da wannan, kun ji cewa Mathew Akawu, dan takarar majalisar dokokin jiha a Plateau, karkashin jam'iyyar PDP na mazabar Pengana ya riga mu gidan gaskiya.

An rahoto cewa Akawu ya rasu ne a wani asibiti a safiyar ranar Juma'a 6 g watan Janairu bayan fama da gajeruwar rashin lafiya, kamar yadda The Punch ta rahoto.

Wata majiya da ke da kusanci da marigayin ta tabbatarwa The Punch rasuwarsa, tana mai cewa ya rasu awanni ne bayan dawowa daga wani taron bikin gargajiya da aka yi a karamar hukumar Bassa a Plateau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel