Dan Takarar Gwamnan Abiya Na Jam'iyyar PDP Ya Kwanta Rashin Lafiya

Dan Takarar Gwamnan Abiya Na Jam'iyyar PDP Ya Kwanta Rashin Lafiya

  • Gwamnan jihar Abiya ya tabbatar da cewa dan takarar dake neman zama gwamna a inuwar PDP ya kwnata rashin lafiya
  • Okezie Ikpeazu ya sanar da cewa dan takarar ya fara samun sauki kuma nan ba da jimawa ba zai dawo cikin tawagar kamfe
  • Jihar Abiya na daya daga cikin jihohin gwamnonin G-5 wadanda ke takun saka da shugabancin PDP da Atiku Abubakar

Abia - Gwamna Okezie Ikpeazu na jihar Abiya ranar Litinin ya tabbatar da cewa dan takarar gwamnan jihar a inuwar Peoples Democratic Party (PDP), Uche Ikonne, ya kwanta rashin lafiya.

Gwamna Ikpeazu ya ba da wannan tabbacin ne a cikin shirin gidan Radiyo, wanda hukumar Dillancin labarai ta kasa (NAN) ta bibiya a Umuahia.

Okezie Ikpeazu na jihar Abiya.
Dan Takarar Gwamnan Abiya Na Jam'iyyar PDP Ya Kwanta Rashin Lafiya Hoto: premiumtimes
Asali: UGC

Ikpeazu ya bayyana cewa Mista Ikonne, "ya fara samun sauki a hankali a hankali kuma yana murmure wa." kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Bidiyon Yadda Aka Ceci Fitaccen Dan Takarar Shugaban Kasa Daga Tulin Jama'a Ya Fito

A cewar gwamnan, dan takarar ya halarci gangamin kamfe da jam'iyar PDP ta shirya a wurare da dama a jihar Abiya, daga ciki har da kaddamar da kamfen jiha baki daya ranar 24 ga watan Nuwamba, 2022.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga nan bayan barin filin wasan Umuahia, Mista Ikonne ya zarce zuwa shagalin Gala da aka shirya domin girmama gwamnonin G-5 a mahaifar gwamna Ikpeazu Umuobiakwa kuma ya samu damar yin jawabi.

Gwamnan Abiya ya ci gaba da cewa:

"Bayan nan ne ya kwanta rashin lafiya, kuma abun ya kai ga kwanciya Asibiti amma ya samu sauki, Ikonne ya fara murmure wa kuma lafiya na kara samuwa. A halin yanzun an sallame shi daga Asibiti."
"Yana bin matakan warwarewa ne a yanzu kuma ina da tabbacin zai warke ya samu karsashi fiye da na baya sannan ya dawo a ci gaba tare da shi."

Kara karanta wannan

Saura Kwana 40 Zabe, Manyan Yan Takara Atiku da Kwankwaso Sun Yi Babban Rashi a Arewacin Najeriya

Gwamna Ikpeazu ya roki mazauna jihar kar su karaya, ya tabbatar masu da cewa nan ba da jimawa ba dan takararsu na gwamna zai wattsake ya koma bakin daga.

Bugu da kari, Ikpeazu yace rashin dan takarar ba zai ragi jirgin yakin neman zaben PDP ba yayin da babban zabe ke kara matsowa.

Ku Hada Kai Ku Zabi Shugabanni Nagari, Sheikh Gumi Ga Musulman Najeriya

A wani labarin kuma Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana muhimman abubuwan da Musulmi na kwarai zasu duba a zabe mai zuwa

Shararren Malamin wanda ya yi kaurin suna wajen haddasa cece-kuce ya roki Musulman Najeriya su sauke nauyin dake kansu na zaben shugabanni nagari.

Yace ya zama dole kowa ya tashi ya zabi shugaba mai tsoron Allah, mai sauraren koken Talata kuma mai girmama Addinin Musulunci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel