Gobara Ta Kama a Dakin Ajiyan Masana’antar Kayan Abinci Na Sumal a Jihar Oyo

Gobara Ta Kama a Dakin Ajiyan Masana’antar Kayan Abinci Na Sumal a Jihar Oyo

  • An samu aukuwar mummunar gobara a jihar Oyo, inda aka samu asarar dukiya mai yawa a wani kamfanin kayan abinci
  • Rahoton da muka samo ya bayyana cewa, gobarar ta kama ne da sanyin safiyar yau Laraba 25 ga watan Janairu
  • Ana yawan samun ballewar wuta ba tare da gano musabbabin hakan ba a yankuna daban-daban na Najeriya

Ibadan, jihar Oyo - Yanzu muke samun mummunan labarin yadda gobara ta kama dakin ajiyan kayayyakin abinci a kamfanin Sumal Foods Limited.

A cewar rahoton Punch, gobarar ta tashi ne a ma’ajiyar kayan abincin kamfanin da ke unguwar masana’antu na Oluyele da ke birnin Ibadan a jihar Oyo.

An ce gobarar ta fara ne da sanyin safiyar yau Laraba 25 Janairu, 2023, kamar yadda rahoto ya bayyana.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Tsohon Gwamnan Adamawa, Jibrilla Bindow, Tare Da Mabiyansa Sun Fita Daga APC

Yadda gobara ta kama kamfani
Gobara Ta Kama a Dakin Ajiyan Masana’antar Kayan Abinci Na Sumal a Jihar Oyo | Hoto: puncnh.com
Asali: UGC

Ya zuwa yanzu dai babu cikakken bayanai na abin da gobarar ta ci da kuma halin da ake ciki na tashin hankali.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda lamarin ya faru

An tattaro cewa, wutar ta fara kamawa ne daga sashen burodi na ma'ajiyar kamfanin na Sumal Foods Limited.

Sai dai, ya zuwa yanzu dai ba a gano musabbabin kamawar gobarar da ake fargabar ta lalata dukiya mai yawa ba.

An girke jami'an tsaro a harabar kamfanin domin tabbatar da tsaro yayin da ake ci gaba da kokarin kashe wutar.

Babban manajan hukumar kashe gobara ta jihar Oyo, Yemi Akinyinka ya tabbatarwa jaridar Punch faruwar lamarin ta wayar tarko.

Asali: Legit.ng

Online view pixel