Dan takarar gwamna a Bauchi ya sauya tunani, Ya koma jam'iyyar PDP

Dan takarar gwamna a Bauchi ya sauya tunani, Ya koma jam'iyyar PDP

  • Ɗan takarar gwamna a jihar Bauchi a zaben watan Maris mai zuwa ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP
  • Auwal Isa tare da ɗumbin magoya bayansa a jam'iyyar APM sun ayyana goyon bayansu ga kudirin tazarcen gwamna Muhammed
  • Shugabar matan APC ta shiyyar arewa maso gabas da shugabar matan NNPP a Bauchi duk sun bi sahu zuwa PDP

Bauchi - Dan takarar gwamna na jam'iyyar APM a jihar Bauchi, Auwal Isah, ya janye daga shiga tseren kuma ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar PDP mai mulkin jihar.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa ɗan takarar ya shiga PDP ne tare da dandazon magoya bayansa, lamarin da ya kawo karshen burinsa na zama gwamna a zaben watan Maris.

Tutar jam'iyyar PDP.
Dan takarar gwamna a Bauchi ya sauya tunani, Ya koma jam'iyyar PDP Hoto: leadership
Asali: UGC

Isah, wanda ya sanar da ci gaban a Darazo, ya kuma ayyana goyon baya da mubaya'a ga kudirin neman tazarcen gwamna Bala Muhammed na PDP

Kara karanta wannan

2023: Wata Ɗaya Kafin Zabe, Atiku da PDP Sun Samu Gagarumar Nasara a Jihar Tinubu

Meyasa ya janye daga neman gwamna?

A cewarsa, ya yanke shawarar jingine tikitin takararsa da kuma haɗe wa da tawagar kamfen Kauran Bauchi saboda burinsa na ganin Bauchi ta samu cigaba duba da kokarin gwamnan ke yi a jihar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yace ayyukan da gwamnan ya zuba wanda ido ke iya gani kamar samar da ruwa, Tituna, kiwon lafiya, makarantu, wutar lantarki da sauransu na cikin abinda suka kalla suka ga ya dace su marawa PDP baya.

Jiga-jigan APC sun bi sahu zuwa PDP

Baya ga wannan ci gaban, shugaban matan APC ta ƙasa reshen shiyyar arewa maso gabas, Amina Manga, shugabar matan NNPP ta Bauchi ta tsakiya, Hajiya Zulaihatu Darazo, sun sanar da komawa PDP.

A cewar manyan yan siyasan sun ɗauki wannan matakin ne ganin yadda mata ke samun fifiko a gwamnatin Bala Muhammed na Bauchi.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Bayan Gazawar APC da PDP, Yan Najeriya Suna da Wani Zabi Ɗaya Rak

A wani labarin kuma Hadimin Gwamna, Sakataren APC da Wasu Jiga-Jigai Sun Fice Daga Jam'iyar zuwa NNPP a Gombe

Wata ɗaya gabanin zabe, jam'iyyar APC ta ƙara tarwatsewa a jihar Gombe yayin da mai ba gwamna mai ci shawara, Sakataren APC da wasu kusoshin sun fice daga inuwarta. Sun koma NNPP mai kayan alatu, sun ce ya kamata yan Najeriya su yi koyi da su wajen haɗa karfi a jam'iyya mai kayan marmari a kawar da APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel