'Yan Ta'adda Sun Kashe Mutum 3, Sun Sace Wasu A Babban Jihar Arewa

'Yan Ta'adda Sun Kashe Mutum 3, Sun Sace Wasu A Babban Jihar Arewa

  • Wasu mahara sun afka wasu kauyuka a karamar hukumar Shiroro an jihar Neja sun halaka mutane uku
  • Maharan kuma suna sace wasu al'umma, sun jikkata wasu kuma sun sace shanu da kayan abinci daga rumbu
  • Kwamishinan tsaron cikin gida da jin kai na Neja, Emmanuel Umar ya tabbatar da harin ya ce fararen hula da jami'an tsaro sun jikkata

Neja - Wasu yan ta'adda sun kai hari garin Gwada da ke karamar hukumar Shiroro na jihar Neja inda suka kashe mutum uku suka sace wasu.

Premium Times ta rahoto cewa maharan sun kai hari kauyuka bakwai a yankin hakan ya tilasta wa mutane tserewa daga gidajensu zuwa makarantar sakandare ta Gwada.

Taswirar Neja
'Yan Ta'dda Sun Kashe Mutum 3, Sun Sace Wasu A Babban Jihar Arewa. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Uwa Ta Fasa Asusun Yaranta Bayan Shekaru 10, Ta Fitar Da Tsoffin Kudi a Bidiyo

Salis Sabo, mai magana da yawun hadakar kungiyoyin Shiroro (COSA) ya ce harin ya wuce awa biyar.

Ya kara da cewa:

"Yan bindigan sun shiga kauyuka fiye da bakwai, suna harbi, mutane da dama sun yi rauni yayin kokarin tserewa.
"Sun kai hari kauyuka kamar Chiri, Kadna, Kam, Vemu da wasu kauyuka da kan hanyar Zumba-Gwada na tsawon fiye da awa biyar ba tare da taimako daga kowa ba ko jami'an tsaro."

Mr Sabo ya ce shugaban karamar hukumar Shiroro, Akilu Kuta, da kyar ya tsira da shima an sace shi, yana mai cewa yan ta'adan sun kashe kansila na Allawa, rahoton The Nation.

A cewar Mr Sabo an sace wata mata da surukarta a garin Bmanape, yayin da mutum na uku a Kadna aka sace ta.

Dalilin kai harin

Anyi imanin cewa an kawo harin ne domin sace shanu. Amma, a yayin kokarin tafiya da shanun, maharan suka tare babban hanyar kauyen Egwa inda suka halaka mutane da dama.

Kara karanta wannan

Kaico: An shiga tashin hankali, 'yan bindiga sun sace amare 2 da mutum 47 a jihar Arewa

Mr Sabo ya ce yan ta'addan sun kwashe abinci daga rumbunan yan kauyen sun kuma sace akuyoyi masu yawa.

Ya bukaci gwamnati ta kara jajircewa wurin kiyayye rayuka da dukiyoyin al'umma.

Kwamishinan tsaron cikin gida ya tabbatar da harin

Da aka tuntube shi, kwamishinan tsaron cikin gida da jin kai, Emmanuel Umar, ya tabbatar da harin, ya ce fararen hula biyu da jami'an soja sun jikkata.

Kwamishinan ya ce:

"Ba mu riga mun tabbatar da ainihin adadin wadanda suka rasu ba, amma zan iya fada mata cewa an harbi wasu jami'an tsaron mu yayin fafatawa da maharan."

Yan ta'adda sun kona babban faston darikar katolika a Jihar Neja

A wani rahoton kun ji cewa wasu yan bindiga sun halaka babban malamin addinin kirista Rabaran Fada Isaac Achi yayin harin da suka kai gidansa cikin dare.

Kamar yadda Daily Trust ta rahoto, maharan sun gaza shiga cikin gidan su cimmasa hakan yasa suka banka wa gidan wuta kuma hakan ya yi sanadin rasuwarsa.

Kara karanta wannan

Kano: Rayuka 2 na Matasan da Suka je Gyara Sokaway a Kano Sun Salwanta Bayan Sun Kasa Fitowa

Asali: Legit.ng

Online view pixel