'Yan Ta'adda Tafi Har Gida Sun Ƙona Babban Malamin Addini Da Ransa A Jihar Arewa

'Yan Ta'adda Tafi Har Gida Sun Ƙona Babban Malamin Addini Da Ransa A Jihar Arewa

  • Wasu gungun yan bindiga sun aikata babban ta'addi a Daza road, Kafin-Koro, karamar hukumar Paikoro, ta Jihar Neja a ranar Lahadi, 15 ga watan Janairu
  • Yan bindigan sun kona Rabaran Fada Isaac Achi, limamin katolika, ta ransa yayin da suka gaza shiga gidansa
  • Rahotanni sun bayyana cewa yan bindigan sun harbi wani takwaran Rabaran Achi, Fada Collins, kuma yana can ana masa magani a asibiti

Jihar Neja - Wasu yan ta'adda sun halaka Rabaran Fada Isaac Achi, babban faston katolika yayin da suka kai hari gidansa misalin karfe 3 na daren Lahadi, rahoton The Nation.

Daily Trust ta tattaro cewa bayan maharan sun gaza shiga gidansa saboda kofofin, sun yanke shawarar cinnawa gidan wuta kuma faston yana ciki.

Rabaran Isaac
'Yan Ta'adda Tafi Har Gida Sun Ƙona Babban Malamin Addini Da Ransa A Jihar Arewa. Hoto: Nigeria Catholic Network
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Fitaccen Malami a Najeriya

Kafin rasuwarsa, Achi ne babban fasto da ke kula da cocin St Peters da St Paul, Kafin Koro, a karamar hukumar Neja.

Kakakin yan sandan jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun ya tabbatar da afkuwar lamarin, ya kuma ce an harbi wani faston yayin harin.

A sanarwar da ya fitar, Abiodun ya ce:

"A ranar 15/01/2023 misalin karfe 3 yan bindiga sun kutsa gidan wani Rabaran Fada Isaac Achi na cocin St Peters da St Paul na katolika, kan Daza road, Kafin Koro, karamar hukumar Paikoro.
"Yan bindigan sun yi yunkurin shiga gidan amma sun kasa sai suka cinnawa gidan wuta, yayin da rabaran fadan ya mutu.
"An kuma harbi wani rabaran fada Collins a kafada yayin da ya ke kokarin tserewa daga gidan. An tura yan sanda da ke Kafin-Koro wurin amma maharan sun tsere kafin isowarsu.
"An gano gawar Fada Isaac yayin da an garzaya da Fada Collins asibiti don masa magani."

Kara karanta wannan

Magoya Bayan PDP Da Dama Sun Mutu Sakamakon Hatsarin Mota A Shahararriyar Jihar Arewa

Kwamishinan yan sandan Neja, CP Ogundele Ayodeji ya tura karin tawagar yan sanda wurin a kokarin kamo maharan kuma an fara bincike.

Yan Ta'adda Sun Sace Malamin Addini a Jihar Ekiti

A bangare guda, wasu mahara sun sace babban malamin addinin kirista a jihar Ekiti, Rabaran Fada Michael Olofinlade.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa yan bindigan da ake zargin masu garkuwa ne sun sace malamin ne a Omu Ekiti, karamar hukumar Oye na jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel