Sun Shafe Tsawon Shekaru 10 Suna Ajiyar Kudi: Uwa Ta Fasa Asusun Bankin Yaranta

Sun Shafe Tsawon Shekaru 10 Suna Ajiyar Kudi: Uwa Ta Fasa Asusun Bankin Yaranta

  • Shararriyar mai gabatar da shirye-shirye a TVC, Morayo Afolabi Brown, ta fasa asusun bankin yaranta wanda suke amfani da shi tsawon kimanin shekaru 10
  • Morayo ta bayyana cewa ta kwashe kudaden ciki don su iya sauya su zuwa sabbin kudin da CBN ya saki
  • Mutane da dama da suka yi martani sun sha mamakin yadda yaran suka jajirce wajen koyon dabi'ar ajiyar kudi

Wata yar jarida kuma mai gabatar da shirye-shirye, Morayo Afolabi Brown, ta saki wani bidiyon kudin da yaranta ke tarawa kusan shekaru 10.

A wata wallafa da ta yi a Instagram a ranar Litinin, 23 ga watan Janairu, uwar ta bayyana cewa ta fasa dakkanin asusun bankinsu. An gano nN500 da N1000 jibge a kasa.

Morayo da tsoffin kudi
Sun Shafe Tsawon Shekaru 10 Suna Ajiyar Kudi: Uwa Ta Fasa Asusun Bankin Yaranta Hoto: @morayobrown
Asali: Instagram

Wa'adin daina amfani da tsoffin kudi na CBN

Morayo ta bayyana cewa za ta kai kudaden banki kasancewar babban bankin kasa wato CBN ya ce za a daina amfani da su.

Kara karanta wannan

Soyayya Ta Gaskiya: Bidiyon Wani Bature da Matarsa Bakar Fata Da Suka Shafe Shekaru 45 da Aure Ya Yadu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mutane da dama da suka ga bidiyon sun sha mamakin cewa yara na iya daukar tsawon lokaci haka suna ajiyar kudi.

Kalli bidiyon kasa:

Jama'a sun yi martani

moscakery ya ce:

"Ba zan iya ajiye kudi a kolo na tsawon watanni 2 ba ba tare da na fasa shi ba, irin wannan horo mai kyau haka."

sweetbakesandevents ta ce:

"Kimanin shekara me? Lokaci na karshe da na yi amfani da kolo ya kasance a 2020, mijina ya fasa asusuna sannan ya samu karfin zuciyar siya mun abubuwa da shi."

boshdesigns ta ce:

"Nima sai da na aikata haka ooo...na mayar da kudin asusun ajiyarsu na banki...amma suna ta tambayata kudinsu na asusu."

princepesa29 ya ce:

"Najeriya ta sha banban da sauran kasashe a kasar a abubuwa da dama. A UK, bayan shekaru 20 za su ci gaba da karba."

Kara karanta wannan

Bidiyon Baturiya Tana Yawo a Hargitse Babu Takalmi a Lagas Ya Girgiza Intanet, Bidiyon Ya Yadu

Iyayen amarya sun ki karbar tsoffin kudi a matsayin sadakinta

A wani labarin kuma, mun ji cewa dangin wata budurwa sun mayarwa iyayen maneman aurenta da kudin sadakinta da suka kawo saboda kasancewarsu tsoffin kudade.

Iyayen yarinyar sun ce ba su da asusun banki da za su iya kai kudin kuma ba su shirya kashe su ba kafin ranar 31 ga watan Janairu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel