'Yan Ta’addan ISWAP da Boko Haram Sun Yi Kazamin Fada, Wasu Sun Mika Wuya Ga Soji

'Yan Ta’addan ISWAP da Boko Haram Sun Yi Kazamin Fada, Wasu Sun Mika Wuya Ga Soji

  • Rundunar sojin Najeriya ta karbi wasu manyan 'yan ta'addan Boko Haram da suka mika wuya a jihar Borno
  • 'Yan ta'addan ISWAP da Boko Haram sun yi kazamin fada a wani dajin Bama a jihar Borno da ke Arewa maso Gabas
  • Ana ci gaba da ganin yadda 'yan ta'addan Boko Haram da ISWAP ke mika wuya ga rundunar sojoji

Bama, jihar Borno - Wata babbar kitmurmurar rikici da ta taso tsakanin ‘yan ta’addan Boko Haram da ISWAP ta yi sanadiyyar mutuwar rayuka da dama a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

An tattaro cewa, ‘yan ta’addan ISWAP ne suka kai farmakin daukar fansa kan na Boko Haram a yankin Mantari da Maimusari da aka fi sani da Gaizuwa a karamar hukumar Bama ta jihar Borno.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar APC Ta Fallasa Naja’atu, Ta Tona Ainihin Dalilin Komawarta Wajen Atiku

A cewar rahoton Zagazola Makama, fadan ya kai ga mutuwar mataka tare da lalata kayayyakin amfanin gida na tsagerun a ranar 22 ga watan Janairun 2023.

'Yan ta'addan Boko Haram sun mika wuya ga sojoji a Borno
'Yan Ta’addan ISWAP da Boko Haram Sun Yi Kazamin Fada, Wasu Sun Mika Wuya Ga Soji | Hoto: ZagazOlaMakama
Asali: UGC

Wata majiya ta shaida cewa, ‘yan ta’addan na ISWAP sun yi nasarar lallasa mayakan Boko Haram, lamarin da ya sa suka fito daga maboyarsu a cikin dajin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

'Yan ta'adda sun mika wuya ga sojoji

Wannan lamari dai ya sa da yawan ‘yan ta’addan ciki har da yara da matansu suka ajiya makamai tare da mika kai ga jami’an tsaro.

Majiyar ta bayyana cewa, daruruwan ‘yan ta’addan ne ciki har da kwamandojinsu da suka tsorata a fagen daga suka mika kai ga jami’an rundunar Operation Hadin Kai da ke Konduga da Banki a jihar, Sahara Reporters ta ruwaito.

Ana ci gaba da samun rahotanni daga majiyoyi na yadda ‘yan ta’addan Boko Haram da ISWAP ke ci gaba da kashe juna saboda tsamin zama.

Kara karanta wannan

Yahaya Bello ya saki layin Tinubu? Gaskiya ta fito daga bakinsa, ya bayyana komai

A bangare guda, rundunar sojin Najeriya na ci gaba da ragargazar ‘yan ta’addan a yankuna daban-daban na Arewa maso Gabas.

Fadawan Shehun Borno 4 Sun Kone Kurmus a Wani Mummunan Hatsarin Mota

A wani labarin kuma, wasu fadawan mai martaba Shehun Borno sun riga mu gidan gaskiya a wani hadarin mota.

Wannan mummunan lamarin ya faru ne a hanyar Maiduguri zuwa Damaturi yayin da motar da suke ciki ta kama da wuta.

An kuma bayyana cewa, akwai wasu mutum uku da suka samu munanan raunuka ta sanadiyyar wannan hadarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel