Zamu Girgiza Kwankwaso a Jihar Kano, Jam’iyyar APC Ta Sha Alwashin Kassara NNPP

Zamu Girgiza Kwankwaso a Jihar Kano, Jam’iyyar APC Ta Sha Alwashin Kassara NNPP

  • Jam’iyyar APC a jihar Kano ta sha alwashin kawo karshen siyasar Kwankwaso a zaben 2023 mai zuwa
  • Wannan na fitowa ne daga bakin wani na kusa da gwamna Abdullahi Umar Ganduje mai mulkin jihar
  • Kwankwaso ne dan takarar shugaban nasa na NNPP, ‘yan APC sun ce za su ba shi mamaki a zaben mai zuwa

Jihar Kano - Jam’iyyar APC mai mulki a jihar Kano ta ce ta gama shiri don ba dan takarar shugaban kasa a NNPP, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso da magoa bayansa mamaki a zaben 2023.

A cewar jam’iyyar ta su Ganduje, mambobinta a jihar za su ba da Kwankwaso mamaki ta hanyar nuna goyon baya ga APC a zaben na shugaban kasa.

Wannan na fitowa ne daga bakin kakakin tawagar kamfen dan takarar gwamnan APC kuma kwamshinan yada labarai na jihar Kano Kwamared Muhammad Garba a wata tattaunawa da Vanguard.

Kara karanta wannan

NNPP Ta Ruɓe, An Bayyana Wanda Ya Kamata Kwankwaso Ya Janye Wa Takarar Shugaban Ƙasa a 2023

Kwankwaso zai sha mamaki a hannunmu, inji 'yan APC a Kano
Zamu Girgiza Kwankwaso a Jihar Kano, Jam’iyyar APC Ta Sha Alwashin Kassara NNPP | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Ya bayyana cewa, jam’iyyar APC na samun goyon baya daga masoya a jihar gabanin zaben mai zuwa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kwankwaso dan Kano ne, amma ba zai samu kuri’unta ba

Da yake jawabi game da Kwankwaso, Garba ya shaidawa jaridar cewa:

“Tabbas Kwankwaso dan Kano ne, da gwamna ne, tsohon minista kuma sanata, tabbas, zao samu ‘yan kuri’u, ba zance ba zai samu kuri’a ba, tabbas zai samu kuri’u kadan, amma APC za ta lallasa shi a zaben shugaban kasa kuma za ta lallasa dukkan sauran jam’iyyun siyasa da yardar Allah a zaben gwamna ma.
“Wannan yasa muka ce za a samu bambanci mai fadi a tsakani a zaben mai zuwa.”

A bangare guda, ya yi watsi da duk waus batutuwa da ke cewa jam’iyyar ta APC za ta yi magudi a zaben da ke tafe nan da wata guda.

Kara karanta wannan

Kyau Kwankwaso Ya Hakura – Kungiya ta Kawo Hujjoji Kan Wanda Arewa Za Ta Zaba

Kwankwaso a yi rashin jiga-jigan NNPP a jihar Bauchi

A wani labarin kuma, kun ji yadda shugaba kuma jagoran tafiyar NNPP a Arewacin Najeriya ya lallaba ya fice daga NNPP tare da kama tafiyar PDP.

An ruwaito cewa, akalla mutum miliyan 2.8 ne suka bar NNPP zuwa yanzu, sun koma wasu jam'iyyun siyasa.

Kwankwaso na ci gaba da bayyana sha'awarsa ta gaje Buhari a zaben da ke tafe nan da wata guda mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel