Mambobin NNPP 700,000 a Bauchi Sun Sauya Sheka Zuwa PDP, Sun Shawarci Kwankwaso Ya Bi Atiku

Mambobin NNPP 700,000 a Bauchi Sun Sauya Sheka Zuwa PDP, Sun Shawarci Kwankwaso Ya Bi Atiku

  • Wani jigon jam’iyyar NNPP ya bayyana sauya sheka zuwa PDP, ya fadi irin asarar da jam’iyyar ta yi a shekarar nan
  • Dr Babayo Liman ya bayyana shawarinsa ga dan takarar shugaban kasa na NNPP da ya lallaba ya marawa Atiku baya
  • Ya kuma shawarci sabbin mambobin na PDP da su kauracewa sanya jar hular ‘yan Kwankwasiyya a nan gaba

Jihar Bauchi - Akalla mambobin jam’iyyar NNPP 700,000 ne suka sau ladansu a jihar Bauchi, suka koma jam’iyyar PDP mai mulkin jihar, rahoton jaridar Leadership.

Hakazalika, mambobin jam’iyyar sama da miliyan biyu da dubu dari takwas ne a jihohin Arewa maso Gabas suka sauya sheka zuwa PDP, a cewar sakataren shiyyar na NNPP, Dr Babayo Liman.

Dr Liman ya bayyana hakan ne a wani taron ‘yan jarida a Bauchi, inda yace miliyan 2.8 daga mambobi miliyan 3.5 da ya yiwa rajista a jam’iyyar cikin shekaru takwas sun kauracewa jam’iyyar.

Kara karanta wannan

2023: Sabon Matsala Ga Kwankwaso Yayin Da Yan NNPP 700,000 Suka Koma PDP a Jihar Arewa, Sun Bada Dalili

Manyan mambobin NNPP sun sauya sheka zuwa PDP
Mambobin NNPP 700,000 a Bauchi Sun Sauya Sheka Zuwa PDP, Sun Shawarci Kwankwaso Ya Bi Atiku | Hoto: withinnigeria.com
Asali: UGC

Da yake jawabi ga manema labarai, Dr Babayo ya shaida cewa, a yanzu dai ya ajiye kujerarsa ta sakaren NNPP a Arewa maso Gabas da kuma mukamin kodinetan Kwankwasiyya na jihar Bauchi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Liman ya bayyana cewa, a hukumance ya yi murabsu ne a ranar 14 ga watan Janairun 2023, amma ya fada a fili ga kowa a ranar Litinin 16 ga watan Janairu, kuma ya koma PDP.

Ka dawo PDP, kiran Dr Liman ga Dr Kwankwaso

Ya yi kira ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da ya dawo jam’iyyar PDP tare da marawa Atiku baya a zaben 2023 don ciyar da Najeriya gaba.

Hakazalika, ya yi kira ga sauran mambobin jam’iyyar a shiyyar Arewa maso Gabas da su dawo PDP, tare da cewa, Atiku ne shugaban siyasar da zai ceto Najeriya daga rikicin tattalin arziki da na siyasa har ma da rashin tsaro, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban PDP, Dan Majalisa da Wasu Kusoshi Sun Bar Tafiyar Atiku, Sun Koma Kwankwaso

Ya kuma shaidawa manema labarai cewa, zai yi murabus ne tare da sauran manyan jiga-jigan jam’iyyar a yankin da suka hada da shugabar matan yankin, Hajiya Halima Tafawa Balewa da sakataren yada labarai na yankin Ibrahim Abdu.

Hakazalika da wani mamban tawagar gangamin kamfen ta Kwankwaso, Tijjani Hassan da dai wasu manyan jiga-jigan masu fada a ji a yankin.

Ku daina sanya hular ‘yan Kwankwasiyya

Dr Liman ya bukaci dukkan wadanda suka sauya sheka zuwa PDP da su daina sanya jar hula ta ‘yan Kwankwasiyya kwata-kwata.

Ya kara da cewa

“Ina amfani da wannan damar don ba mai Sanata Rabiu Musa Kwakwaso da ya marawa Atiku baya don biyan bukatun dukkan ‘yan Najeriya.”

A daidai wannan lokacin ne kuma Kwankwaso ya samu karbuwa a yankin Arewa ta tsakiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel