Iyayen Budurwa Sun ki Karbar Doya 400 na Sadaki Saboda 1 ta Karye, Sun Hana Auren

Iyayen Budurwa Sun ki Karbar Doya 400 na Sadaki Saboda 1 ta Karye, Sun Hana Auren

  • Wani biki a wata jihar gabashi a Najeriya ya watse saboda abubuwan da ya kamata miji ya kawo na kayan auren amarya
  • Dangin amaryar tasa sun bukaci manyan doyoyi 400, amma suka yi watsi da kayayyakin yayin da ya kawo saboda wani dalili daya
  • Don shawo kan lamarin, dangin matar sun yanke shawarar dora masa wani nauyin gaggauta kawo wani abu idan har yana so a yi auren

Wani mutumi 'dan Najeriya ya labarta yadda aka fasa auren 'dan uwansa a jihar Imo saboda doyoyin da aka gabatar a matsayin kayayyakin aure.

Kayan sadaki
Iyayen Budurwa Sun ki Karbar Doya 400 na Sadaki Saboda 1 ta Karye, Sun Hana Auren. Hoto daga Nairametrics
Asali: UGC

@Foedosa1 ya bayyana yadda lamarin ya auku a dandalin Twitter yayin martani ga wani fitacce, John Doe, wanda yayi jinjina ga jihar Edo a matsayin inda yafi ko ina saukin sadaki a Najeriya.

Kara karanta wannan

Kamfen zub da jini: An sheke wani, da dama sun jikkata a kamfen PDP a wata jihar APC

A cewar @Foedosa1, dangin matar da 'dan uwansa zai aura sun bukaci a basu manyan doyoyi 400 a matsayin kayayyakin aure.

Sai dai, suna kan hanyarsu na zuwa kauyen don gabatar da doyoyin, daya daga ciki ta tsage. Ga mamakinsu, dangin matar suka ki amsar duka doyoyin, inda suka tsaya kan cewa dole ya canza wannan tsagaggar doyar da wata a kasuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilinsu kuwa shi ne, matar da za su aura masa ba karyayyar kafa gareta ba.

Martanin jama'a

@Ebonyxtiano ya ce:

"Agba ka na magana ne kan jarin kayan aure ko sadaki? Sadakin amarya ba matsala bane, sadakin kanwata N10,000 ne, mun cire 3,000 mun mikawa surikarmu don ta kula mana da 'diyarmu."

@GeoLawrence1 ta ce:

"Wasu jihohin za su bukaci a kalla N5,000. Amma su bukaci a kalla doyoyi 400. Katuwar doya a wasu wuraren ta kai N1,600 ko kusan haka ( a kasuwar yanzu).

Kara karanta wannan

Kyakkyawar Budurwa Ta Auri Mai Nakasu Bayan Ta Rabu Da Attajirin Saurayinta

" 1,600 sau 400 yafi sama da rabin Naira miliyan. "Oshi!"

@TabiythaOkenwa ta ce:

"Amma fa a koda yaushe ina tambayar kaina wannan tambayar duk lokacin da na gani ko na ji wani abu irin haka. Tambayar ita ce me za su yi da doyoyi 400. Ko suna shirin siyar da su ko kuwa? Zan yi wannan tambayar idan ni amaryar ce na rantse."

@ayinla_mayowa1 ta ce:

"Amma yallabai, ina so in tambaya, me yasa wasu dangin suke yin haka? Ko dai suna yi ne da gangar don tunzura kokarin mutumin wajen auren 'diyarsu ko kuma ketarsu ne na tatse duk wani kudi da ke aljihun mutumin?"
  • Matar aure ta ki karbar motar da 'danta ya bata, ta sanar da dalili

A wani labari na daban, wata matar aure 'yar Najeriya ta ki karbar dalleliyar motar da 'dan ta bata saboda tace bashi da aiki.

Ta fara tuhumarsa aikin da ya ke yi inda ta fusata tare da zuwa ta farfasa balan-balan din da ya saka a motar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel