Yara Na Uku Kowa Ubansa Daban, Wata Budurwa Ta Fashe Da Kuka A Bidiyo

Yara Na Uku Kowa Ubansa Daban, Wata Budurwa Ta Fashe Da Kuka A Bidiyo

  • Wata matashiyar mata wacce ba ta wuce shekaru 20 da yawa ba ta nuna damuwarta kan rashin samun miji
  • Matashiyar, wacce ta yi ikirarin tana da 'ya'ya uku kuma kowane mahaifinsa daban, tace a watan Fabrairu zata cika 24
  • Masu amfani da kafafen sada zumunta sun yi kokarin rarrashinta yayin da wasu 'yan mata suka bayyana halin da suke ciki

Wata matashiya yar shekara 23 ta ja hankalin mutane a shafin TikTok bayan ta bayyana cewa 'ya'ya uku ta haifa amma kowanensu ubansa daban.

A wani bidiyo da aka hangi tana zubda hawaye, budurwar ta ce a watan Fabarairu mai zuwa na 2023 zata cika shekara 24 a duniya amma har yanzun ba ta da aure.

Matashiya.
Yara Na Uku Kowa Ubansa Daban, Wata Budurwa Ta Fashe Da Kuka A Bidiyo Hoto: @shemababy
Asali: UGC

Bidiyon da ta wallafa wanda ta ba da labarain halin da take ciki ya ja hankali mutane da yawa, sama da mutane 500k ne suka kalla.

Kara karanta wannan

Babu Ruwanmu da NEPA: Budurwa Ta Nunawa Duniya Katafaren Gidan Iyayenta a Bidiyo, Jama'a Sun Shiga Mamaki

Da yawan waɗanda suka yi martani game da halin da take ciki sun bata shawari tare da ƙara mata kwarin guiwa ta ƙara hakuri.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Legit.ng Hausa ba ta iya tabbatar da ikirarin matashiyar ba har zuwa yanzun da muke harhaɗa maku wannan rahoton.

Duba bidiyon matar a nan

Martanin jama'a a soshiyal midiya

crowns225 ya yi martani da cewa:

"Ki daina kuka yar uwa, yara kyauta ce daga Allah, ba duk abinda mutum yake so yake samu ba, ki ci gaba da Addu'a komai zai koma daidai."

Ur Ex Girlfriend ta rubuta cewa:

"Lallai ni a wata mai zuwa zan cika shekara 29 a duniya kuma ban taɓa kuka kan haka ba. Ki nemi kuɗi kawai ki kaunaci kanki."

Marymercy49 ta ce:

"A shekaran nan zan cika shekaru 28 ina da ɗa guda ɗaya kuma ni kaɗai ke daukar nauyinsa, kina bukatar karin kwarin guiwa yar uwa."

Kara karanta wannan

Ko da ne ga dan siyasa: Bidiyon mahaukaciyar da ta haifi jariri a kasuwa ya bar baya da kura

A wani labarin kuma Kwana Hudu da Aure, Amarya Ta Kama Angonta da Yar Uwarta Suna Jin Dadi a Gado

Sabuwar amaryan tace abinda ta gani wanda bata taɓa tsammani ba ya fasa mata zuciya ta yadda ta killace kanta a dakin Otal tsawon mako ɗaya, ba wanka ba yawo.

A cewarta, ta garkame lambobin mahaifiyarta da Surukarta saboda sun nemi ta yafe wa mijin da yar uwarta kuma ba ta tunanin zata iya hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel