Daga Kammala Digiri, Matashiya Ta Ce Babu Zama, Ta Kama Sana’ar Dinki Gadan-Gadan

Daga Kammala Digiri, Matashiya Ta Ce Babu Zama, Ta Kama Sana’ar Dinki Gadan-Gadan

  • Wata mata ‘yar Najeriya ta saki komai domin cika burinta na zama tela, ta yi hakan ne bayan zama cikakkiyar lauya
  • Maryam Folashade ta yada bidiyo a TikTok, inda ta nunawa duniya yadda ta fara sanar dinki, abin da take so a ranta
  • Bidiyon da ya yada ya jawo cece-kuce a kafar sada zumunta, jama’a da yawa sun yi martani mai daukar hankali

Wata lauya ‘yar Najeriya ta yi watsi da takardar digirinta na lauya don kawai ta kama burinta na zama mai tela.

Matar mai suna Maryam Folashade ta ce ta shafe shekaru bakwai tana karatun lauya a jami’a, amma ta yanke shawarin zama tela kawai.

A bidiyon da ta yada, an ga Maryam na zaune a cikin wani shago, ga kuma kekunan dinki a ciki.

Daga lauya ta koma sana'ar dinki
Daga Kammala Digiri, Matashiya Ta Ce Babu Zama, Ta Kama Sana’ar Dinki Gadan-Gadan | Hoto: @maryam_folashade.
Asali: UGC

Bidiyon lauyar da ta zama tela

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Uwa Ta Goya Yara 2 a Lokaci Guda Ya Dauka Hankali, Mutane Sun Jinjina Mata

Yayin da ta taka kafa a shagon, matashiyar ta zauna kan keke guda daya kamar dama abin da take jira kenan a rayuwarta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta rubuta a kan bidiyon cewa:

“Gaskiya game da ni. Ni lauya ce mai matukar sha’awar sana’ar dinki.”

Murna da farin ciki a fuskarta ya nuna cewa, tana kaunar wannan sana’a da ta kama.

‘Yan TikTok da suka ga bidiyon sun yi mamaki, amma suka ce ta yanke shawarin da ya dace game da rayuwarta.

Kalli bidiyon:

Martanin jama’a

Ga kadan daga abin da mutane ke cewa:

@Torlorunfe:

"Bayan shekaru 5 a makaranta, ina koyon sana’ar kitso yanzu.”

@Ammy:

"Nima abin da nake shirin yi kenan.”

@user9966297060410:

"Mai digiri a malanta amma kuma yanzu mai sana’ar kitso. Babu abin da zai tsayar damu sai mun kai ga nasara.”

Kara karanta wannan

Budurwa Mai Yara Uku Kowane Mahaifinsa Daban Ta Fashe da Kuka a Bidiyo, Tace Aure Take So

@Godisthebestoption:

"Bayan zama cikakken lauya yanzu sana’ar kitso nake.”

@bigbabybeni:

"Mahaifiyata na zaton ina da taurin kai da nake maganar cewa ina haba-haba na kammala digiri domin shiga makarantar dinki.”

Mai sana’ar wanke-wanke ya fadi yadda sana’arsa take

A wani labarin kuma, wani matashi ya ba da mamaki yayin da bayyana sana’ar da yake yi a kasar waje.

Ya ce ya tafi kasar Jamus, kuma ya kama sana’ar wanke-wanke, kana yana samun abin kansa cikin sauki.

Ya bayyana irin jajircewar da ake bukata a wannan aikin nasa da kuma yadda yake fama da masu gidansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel