Kowa Ya Rasa Mahaifiya Ya Yi Kuka: Wata Uwa Ta Goya Yaranta 2 Reras Da Zani a Bidiyo, Jama’a Sun Yaba Mata

Kowa Ya Rasa Mahaifiya Ya Yi Kuka: Wata Uwa Ta Goya Yaranta 2 Reras Da Zani a Bidiyo, Jama’a Sun Yaba Mata

  • Wata uwa ta sha ruwan yabo saboda karfinta lokacin da mutane suka kalli bidiyonta goye dfa yaranta
  • Matar ta jera yaranta su biyu reras a baya a lokaci ta yadda ko wannensu zai kasance cikin farin ciki da walwala
  • Mutane da dama da suka cika da al'ajabin irin karfin da ta yi amfani da shi wajen aikata hakan sun cika ta da addu'a

Wani bidiyo da @adamsmercy685 ya wallafa a soshiyal midiya ya nuno yadda wata uwa ta goya yaranta biyu a lokaci guda a bayanta.

Dauke da murmushi a fuskarta, matar ta rike yaran biyu a tare a bayanta da zani daya. Abun ya burge mutane da dama.

Uwa goye da yaranta
Kowa Ya Rasa Mahaifiya Ya Yi Kuka: Wata Uwa Ta Goya Yaranta 2 Reras Da Zani a Bidiyo, Jama’a Sun Yaba Mata Hoto: TikTok/@adamsmercy685
Asali: UGC

Uwa ta nuna karfin kulawarta ga 'ya'yanta

An gano yaran da aka jera reras sai kace suna zaune a kan kujera cikin walwala yadda mahaifiyar tasu ta jera.

Kara karanta wannan

Bidiyon Baturiya Tana Yawo a Hargitse Babu Takalmi a Lagas Ya Girgiza Intanet, Bidiyon Ya Yadu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mutane da dama sun yi martani ga bidiyon wanda ya yadu sannan suka bayyana cewa wannan shine karon farko da suke ganin mace tana aikata haka.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@nyadzua05 ta ce:

"Wannan ne karo na farko da nake ganin irin haka."

Lamp ta cika da mamaki:

"Ta yaya ta aikata haka? Ban taba gani ba."

Mom and twin kids ta ce:

"Kin tuna mun da lokacin da nake daukar nawa mazan haka. Yanzu shekarunsu 13."

user1920301563097 ta ce:

"Kina da baya mai karfi da har kika iya daukar manyan yara biyu, ni ko daya na dauka baya wuce minti 30."

dushyantsavania ta ce:

"Ban taba ganin irin wannan ba za ki iya nuna mana yadda kika saka su a baya."

Mutalechomba21 ya ce:

"Wow ban taba ganin wannan ba Allah ya albarkace ki."

Kara karanta wannan

Budurwa Mai Yara Uku Kowane Mahaifinsa Daban Ta Fashe da Kuka a Bidiyo, Tace Aure Take So

Matashi ya yi wa iyayensa sha tara ta arziki, ya dankara masu gida a kauye

A wani labari na daban, mun ji cewa jama'a a soshiyal midiya sun jinjinawa wani matashi bayan ya wallafa bidiyon yadda ya sauya tsohon gidan iyayensa a kauye.

Matashin dai ya rushe gidan wanda a ciki ne ya taso sannan ya dankara masu sabo irin na zamani mai dauke da katafaren 'gate' da katanga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel