Yan Bindiga Sun Banka Wa Ofishin Yan Sanda Wuta, Sun Kashe Jami'i 1 a Imo

Yan Bindiga Sun Banka Wa Ofishin Yan Sanda Wuta, Sun Kashe Jami'i 1 a Imo

  • 'Yan bindiga sun kai hari hedkwatar 'yan sanda da abubuwan fashewa a jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya
  • Bayanai sun nuna cewa jami'an tsaron da ke bakin aiki sun yi nasarar dakile harin amma ɗaya daga ciki ya rasa rayuwarsa
  • Mai magana da yawun 'yan sandan jihar ya ce jami'an sun bazama neman maharan

Imo - Jami'in hukumar 'yan sanda ɗaya ya mutu a ranar Jumu'a da daddare lokacin da wasu 'yan bindiga suka kai mummunan hari ofishin 'yan sanda a karamar hukumar Oguta, jihar Imo.

Wakilin jaridar Daily Trust ya tattaro cewa gwarazan dakarun 'yan sanda da ke bakin aiki sun yi nasarar dakili harin 'yan ta'addan yayin musayar wuta.

Harin yan bindiga a Imo.
Yan Bindiga Sun Banka Wa Ofishin Yan Sanda Wuta, Sun Kashe Jami'i 1 a Imo Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Bayan sun yi ajalin ɗan sandan, bayanai sun nuna cewa yan bindigan sun gudu da raunukan harbin bindiga a jikinsu sakamakon artabu da jami'an tsaro.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Ceto Yara 2 Cikin Daliban Jihar Nasarawa 6 Da Yan Bindiga Suka Sace

An ce suna isa Ofishin 'yan sanda, maharan ba su yi wata-wata ba suka fara jefa kayan fashewa da ake zaton bama-bamai ne kana suka bude wa jami'an da ke wurin wuta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sanda a jihar Imo, Henry Okoye, ya tabbatar da kai harin ga manema labarai, ya ce dakaru sun fatattaki yan bindigan.

Ya ce yayin musayar wuta da jami'an da ke kan bakin aikin, maharan sun kwashi kashinsu a hannu, da suka ga karfin luguden wuta ya fi karfinsu sai suka tsere.

Kakakin yan sandan ya ce a halin yanzun jami'an tsaro sun baza komarsu ta ko ina domin damƙo yan ta'addan, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Yace:

"Da safiyar nan jami'ai suka yi artabu da yan bindiga a Hedkwatar Oguta. Maharan sun kwashi kashinsu a hannun mu. Abin yakaici jami'i ɗaya ya rigamu gidan gaskiya."

Kara karanta wannan

An Kama Sarakuna Biyu da Hannu a Garkuwa da Fasinjojin Jirgin Kasa a Najeriya

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa wannan harin na baya ya zo ne ƙasa da mako ɗaya bayan wasu yan bindiga da ba'a san ko su waye ba sun kai farmaki Caji Ofis din Agwa.

Ɗan takarar gwamna ya sha da kyar a Ribas

A wani labarin kuma Miyagu Sun Farmaki Dan Takarar Gwamna a Jihar Ribas, Sun Tafka Barna

Chief Dumo Lulu-Briggs, mai neman zama gwamnan Ribas a Accord Party ya tabbatar da cewa an kai masa hari kuma motar da yake ciki ta lalace.

Ya kara da bayanin cewa ya yi kokarin kiran wayar tarhon kwamishinan yan sanda na jihar Ribas, CP Okon Effiong Okon, amma bisa rashin sa'a lambarsa ta ƙi shiga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel