CBN Zai Ci Tarar Bankuna N1m Kowacce Rana Saboda Kin Karbar Sabbin Takardun Naira

CBN Zai Ci Tarar Bankuna N1m Kowacce Rana Saboda Kin Karbar Sabbin Takardun Naira

  • Babban Bankin Najeriya ya ce ya sanya tara kan bankunan da ke kin daukar sabbin kudade da aka buga a kasar
  • Wannan na zuwa ne daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da kokawa kan karancin sabbin kudaden a bankunan kasar
  • Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da wayar da kan jama’a game da sabbin kudin da kuma lokacin da za a daina amfani dasu

Osogbo, jihar Osun - Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da zai fara daukar matakin cin tara ga bankunan da suka ki zuwa daukar sabbin kudin Naira da ya buga, The Nation ta ruwaito.

A cewar CBN, zai caji duk wani bankin da ya ki zuwa daukar kudin a kowacce rana N1m kan kowane akwatin kudi da suka ki dauka don ba kwastomomi a Najeriya yayin da wa’adin daina kashe tsoffin kudi ke karatowa.

Kara karanta wannan

CBN Ya Zargi Wasu Bankuna Da Ɓoye Sabbin Takardun Naira Har N4.2bn A Wata Jihar Kudancin Najeriya

CBN ta bayyana hakan ne a rana Juma’a yayin taron wayar d akan jama’a game da sabbin kudi a jihar Osun, inda aka yiwa mata da ke wata kasuwa a Ayegbaju bayani kan tsarin sabbin N200, N500 da N1,000.

CBN zai ci bankuna taran N1m kowace rana
CBN Zai Ci Tarar Bankuna N1m Kowacce Rana Saboda Kin Karbar Sabbin Takardun Naira | Hoto: David Darius
Asali: Getty Images

Idan baku manta ba, CBN ya kashe tsoffin N200, N500 da N1,000 tare da kirkirar sabbi a shekarar da ta gabata, an sanya 31 ga watan Janairu a matsayin wa’adin daina amfani dasu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Laifin bankuna ne, mun buga wadatattun kudi, inji CBN

Da yake magana a taron, Mataimakin Daraktan bincike na CBN. Adeleke Adelokun ya bayyana cewa, babban bankin ya buga wadatattun kudi, amma bankuna sun ki dauka, rahoton TheCable.

A cewarsa:

“CBN ya buga wadatattun sabbin Naira amma mun gano da yawan bankuna basu zo sun dauka ba.
“Mun gano sun ki zuwa su dauki sabbin kudin, mun kakaba taran N1m kan kowane akwati da duk wani banki ya ki zuwa dauka a rana ya danganta da adadin kwanakin.

Kara karanta wannan

Gwamnan Barno Yakoka Kan Yadda Sabbin Kudin Da CBN, Ya Shigo Dasu Basa Zagayawa A Tsakanin Al'ummarsa

“Mun kuma umarci a sanya sabbin Naira a dukkan injunan ATM a fadin Najeriya saboda ‘yan kasa su sami damar samun sabbin kudin."

An boye N2.7trn ba a juya su, inji CBN

A bangare guda, mai kula da bankin CBN a Osogbo, Madojemu Daphne, wanda ya samu wakilcin Adebayo Omosolape ya bayyana cewa, ‘yan Najeriya da sun boye tsoffin kudade da suka kai akalla N2.7trn da ba a tabawa.

A bangare guda, CBN ya ce duk wani dan Najeriya da banki ya bashi tsohon kudi kada ya amince ya karba, domin kuwa hakan zai sa a ci gaba da kashe tsoffin kudade.

Asali: Legit.ng

Online view pixel