Barno: Zulum Ya Koka Kan Sabbin Kudin Da CBN, Ya Shigo Da Su

Barno: Zulum Ya Koka Kan Sabbin Kudin Da CBN, Ya Shigo Da Su

  • Gwamnan babban jihar Barno Ya koka kan yarda al'ummarsa ta jihar Barno suka gaza samun sabbin kudi
  • Wa'adin sauyin kudin dai yazo gaf, domin saura kwana goma, kamar yadda babban bankin ya sanar
  • Gwamna Zulum ya bukaci da a duba yiwuwar hanyar da za'a inganta zagayawar kudin a tsakan in al'umna

Barno - Gwaman jihar Barno ya koka kan yadda Sabbin kudin da CBN, ya fito da shi yai karancin ko kuma ya kasa zagayawa a tsakanin al'ummarsa, sabida matsal-tsalun tsaron

Zulum ya fadi hakan ne a a lokacin da kwamitin da ke kula da sake da kuma rarraba sabbin kudi ya kai masa ziyara a ofishinsa dake Maiduguri. Rahoton Vanguard

Zulum ya fadawa yan kwamitin wanda darkatan kididdiga na rashen bankin da ke Maiduguri ya jagoranta

Kara karanta wannan

Gwamnatin Ganduje Ta Jawo Farfesa Jega, Ta Hada Shi da Wani Babban Nauyi a Najeriya

"A cikin hanannan hukumomi ashirin da bakwai da suke maiduguri, guda uku ne kawai a cikin birni, Maiduguri, Jere da kuma Biu sannan a nan kuma akwai bunkuna da suke aiki, amma sauran kanan hukumomin babu bankuna kusan sama da shekara goma, babu turakan sadarwa da sauran kuma wasu abubuwan hada-hada na digital"
Zulum yace duk wadannan abubuwan sun ffn faru ne sakamakon rikicin Boko Haram",

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Zulum ya ci gaba da cewa:

"Gwamnatin jihar Barno zata taimaka wajen bunkasa tare da tabbatar da dokar babban bankin kasa, amma magana gasakiya wannan sabbin kudaden basa zagayawa a tsakanin al'ummar mu“

Zulum
Barno: Zulum Ya Koka Kan Sabbin Kudin Da CBN, Ya Shigo Da Su Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Tunda fara a jawabina, Daraktan Kiddiga na bankin Tumala yace:

"Babban bankin kasa ya umarci dukkanin darakatocin jihohi da su saki kudin kuma su tabbatar da suna zagayawa a tsakanin mutane"

Kara karanta wannan

Tun yanzu Atiku ya fara yiwa mutane alkawarin kwangila, halin mutum bai canzawa: APC

Kuma muma zamu tabbatar da wannan dokar a jihar Barno"

Kudaden zasu zagaya

Kamar yadda kuka sani mu ma yan Barno ne, kuma muna tabbatar muku cewa wannan batun sauyin kudin mun dukufa ganin mun ga sun wadatu a tsakanin al'umma

"Kamar yadda aka sanar da ranar 31 ga watan Janairun nan, shine lokacin da za'a daina mu'amala da tsoffin kudi, tu muna tabbatar maka zamuyi iyaka iyawar mu wajen tabbatar da yawan kudin a cikin injunan cirar kudi na ATM"

Daraktan yace muna nan muna bib iya da kuma tabbatar da an samu ci gaba a wannan tsarin na sauyi da babban bankin kasa ya shigo dashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel