CBN Ya Zargi Wasu Bankuna Da Ɓoye Sabbin Takardun Naira Har N4.2bn A Wata Jihar Kudancin Najeriya

CBN Ya Zargi Wasu Bankuna Da Ɓoye Sabbin Takardun Naira Har N4.2bn A Wata Jihar Kudancin Najeriya

  • CBN ya zargi wasu bankunan kasuwanci da boye sabbin nairori da aka basu ba tare da wani dalili ba wanda zagon kasa ne ga kokarin da babban bankin ke yi na wadatar da al'umma da sabbin kudin
  • Maxwell Okafor, kwantrola na CBN reshen jihar Ribas ne ya yi wannan zargin bayan shi da tawagarsa sun zaga bankuna da kasuwani
  • Okafor ya ce an raba wa bankunan Fatakwal N4.5bn ranar Alhamis da Juma'a amma ba su saka a ATM ba suna boye wa don bawa kwastomomi na musamman

Fatakwal - Babban bankin Najeriya, CBN, ya zargi wasu bankunan kasuwanci a Fatakwal, Jihar Ribas da kin rabar da sabbin takardun Naira da adadin su ya kai Naira biliyan 4.5, Daily Trust ta rahoto.

Kwantrolla na CBN reshen jihar Ribas, Maxwell Okafor, wanda ya jagoranci wata tawaga na masu tabbatar da bin doka kan sabbin nairorin zuwa wasu bankunan kasuwanci da kasuwanni a Fatakwal ne ya yi wannan korafin.

Kara karanta wannan

Tof fa: Bankuna sun Ssabawa CBN game da sabbin kudi, suna ta ba mutane tsoffin kudi a ATM

Sabbin Takardun Naira
CBN Ya Zargi Wasu Bankuna Da Ɓoye Biloyoyin Sabbin Takardun Naira A Wata Jihar Kudancin Najeriya. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce tsakanin ranar Alhamis da Juma'a, babban bankin ya rabar da sabbin kudi N4.5bn ga bankunan kasuwanci a jihar amma yana mamakin dalilin da yasa kwastomomi da dama ba su samu kudin ba.

Bankunan kasuwancin na neman kawo cikas ga kokarin CBN, Okafor

Ya bayyana damuwa kan cewa wasu bankunan a Fatakwal na kawo cikas ga kokarin CBN na rabar da sabbin nairorin ta hanyar ɓoye kudaden a wurin ajiyar kudinsu.

Ya ce:

"Muna sa ido kan rabar da sabbin takardun naira kuma abin da muke gani bai mana daɗi ba. Mun ziyarci wasu bankuna kuma wani cikinsu baya bada sabbin takardun nairan. Injin ATM dinsu baya aiki, tun da wuri da muka tafi. Muna da tabbas cewa bankin ya samu kudi daga CBN. Wasu bankunan sun samu kudi jiya kuma har yanzu suna rufe a dakin ajiye kudi.

Kara karanta wannan

Ana Saura Kwana 11 Tsoffin Kudi su Zmaa Takardun Tsire, Bankuna na Cigaba da Bada Tsofaffin Kudi

"A wasu bankunan, ATM dinsu baya aiki. Babu uzuri kan abin da suke aikatawa. CBN ta yi gargadi cewa akwai hukunci mai tsauri ga wadanda ke boye sabbin nairan don bawa kwastomomi na musamman.
"Mun dena bada tsaffin naira tunda sabbin suka fito. Ba dalilin da zai sa babu kuɗi a ATM; kuma kudin da suka karba yana ajiye. Bankuna suna matsa wa a kara musu kudi, toh me suka yi da wadanda aka basu? Me suka yi da N2.5bn da 2bn da suka karba?
"Za mu kai maganan gaba domin a san matakin da za a dauka a kansu."

Direktan tsare-tsare na CBN, Emenike Chimele, shima ya ce babu shakka wasu bankunan na kokarin kawo cikas ga kokarin da babban bankin ke yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel