Uwar Gidan Atiku Ta Bayyana Wani Abin Mamaki Game Da Gwamnatin Obasanjo
- Uwargidan dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Titi Abubakar, ta bayyana dalilin da yasa ya kamata a zabi mijinta a matsayin shugaban kasa na gaba
- Ta ce mijinta ya sa yadda ake tafiyar da tattalin arziki, ta kara da cewa shine dalilin nasarorin da aka samu a gwamnatin Obasanjo
- Titi Abubakar, wacce ta yi magana a Abeokuta ta ce zaben na 2023 lokacin a yi wa mijinta sakayya ne
Abeokuta, Jihar Ogun - Titi Abubakar, uwar gidan Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ta ce mijinta ne dalilin da yasa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi nasara a gwamnatinsa.
Mrs Atiku ta yi wannan ikirarin ne a ranar Laraba, 18 ga watan Janairu, a ralli na shugaban kasa na PDP da aka yi a fadar Ake a Abeokuta, jihar Ogun, PM News ta rahoto.

Kara karanta wannan
Zaben 2023: Yaƙin Da APC Da PDP Ke Yi Ya Ɗauki Sabon Salo Yayin Da Tinubu Ya Tona Babban Ajandar Atiku

Asali: Facebook
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarta, nasarorin da Najeriya ta samu a bangaren tattalin arziki, masana'antu, samar da ayyuka da sauran bangarori duk saboda tallafi, jajircewa da biyayya irin na mijinta Atiku Abubakar ya yi ne a matsayin mataimakin shugaban kasa.
Zaben shugaban kasa na 2023: Lokacin sakayya ne, in ji matar Atiku
Matar na Atiku ta cigaba da cewa a ranar 25 ga watan Fabrairu da za a yi zaben shugaban kasa ranar sakayya ne ga mijinta ta hannun Obasanjo.
Kalamanta:
"Atiku shine dan takarar shugaban kasa mafi cancanta da ya kamata ku zaba. Ya san yadda ake tafiyar da tattalin arzikin kasar, shine babban dalilin nasarorin da aka samu lokacin mulkin Obasanjo saboda shine mataimakin shugaban kasa.
"Yana da kwarewa kuma ya san abin da ake bukata don tafiyar da kamfanoni, tattalin arziki da sauransu."

Kara karanta wannan
Tonon silili: Tinubu dan ta'adda ne, ina da shaidu a kasa, inji kakakin kamfen Atiku
Katsina sun yi wa Atiku Abubakar gagarumin tattaki na nuna goyon baya
A wani rahoton, kimanin kungiyoyi 74 ne karkashin hadakar 'Arewa Decades' suka shiryawa Alhaji Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, tattakin nuna goyon baya a Katsina.
Rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar da cewa an fara tattakin ne tun daga kwanar Gidan Dawa da Otel din Liyafa a babban birnin jihar Katsina inda kungiyoyin guda 74 daga sassa daban-daban suka halarta.
Asali: Legit.ng