An Shiryawa Atiku Abubakar Wani Gagarumin Tattaki a Katsina

An Shiryawa Atiku Abubakar Wani Gagarumin Tattaki a Katsina

  • Wasu ƙungiyoyin siyasa a jihar Katsina sun shirya tattakin nuna goyon baya ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP
  • Jagoran da ya jagoranci ƙungiyoyin da suka haɗa tattakin yayi Allah wadai da halin da jam'iyyar APC ta jefa ƙasar nan
  • Shugaban PDP na jihar yayi wa Atiku samun ƙuri'u a jihar fiye da ko ina a jihohin ƙasar nan

Aƙalla ƙungiyoyin siyasa 74 ne a ƙarƙashin haɗakar ‘Arewa Decides’, a ranar Juma'a suka shirya tattakin nuna goyon baya a jihar Katsina ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar.

Tattakin goyon bayan wanda aka fara shi tun daga kwanar Gidan Dawa kusa da otal ɗin Liyafa a babban birnin jihar a ranar Juma'a, ya samu halartar ƙungiyoyin siyasa 74 daga sassa daban-daban na jihar. Rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Abokin Takarar Atiku Ya Karaya, Ya Faɗi Wanda Zai Lashe Zaben 2023 Idan G-5 Suka Koma Bayan Tinubu

Atiku Abubakar.
An Shiryawa Atiku Abubakar Wani Gagarumin Tattaki a Katsina Hoto: vanguardngr
Asali: UGC

Da yake zantawa da ƴan jarida jim kaɗan bayan isowar su sakatariyar PDP ta jihar, shugaban haɗakar 'Arewa Decides' na Katsina, Kabir Gambo, ya nuna ɓacin ransa kan yadda abubuwa suka dagule a mulkin APC.

"Tsaro ya tabarbare yunwa, talauci da rashin aikin yi sun yawaita a mulkin jam'iyyar APC," inji shi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar Kabir, haɗakar ta su wacce ke da mabiya ko ina a faɗin jihar, zata nemowa Atiku mutane waɗanda suka cancanci yin zaɓe domin su ƙada masa ƙuri'a a babban zaɓen shugaban ƙasa na 2023 dake tafe.

Shugaban jam'iyyar PDP na jihar, Lawal Magaji, wanda ya samu wakilcin Ibrahim Galadima, ya nuna godiyar sa bisa wannan gagarumin goyon baya da suka nuna wa Atiku da mataimakin sa.

Sannan shugaban ya buƙaci masu zaɓe da su zaɓi PDP daga sama har ƙasa a zaɓen 2023. A kalamansa ya ce:

Kara karanta wannan

Gwamna Tambuwal Ya Bayyana Lokacin Da PDP Zata Yankewa Wike Da Ƴan G5 Hukunci

"Katsina gida ce a wurin Atiku Abubakar na biyu, muna jin ziyarar ku kamar Atiku ne da kan sa ya kawo mana ziyara."
"Muna son mu tabbatar muku da cewa Atiku zai samu ƙuri'u a Katsina fiye da sauran jihohin."

Mu Zamu Yi Nasara Duk Da Ƙawancen G5 da Tinubu -Gwamna Okowa

Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iƴƴar PDP, ya bayyana cewa sune za suyi nasara a zaɓen 2023 dake tafe duk kuwa da shirye-shiryen da ƴan tawagar G5 ke yi na marawa Tinubu baya.

Gwamna Ifeanyi Kowa yace ubangiji shine zai ba su nasara domin haka ba su damu da duk wani hukunci da ƴan tawagar za su yanke ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel