Wacce Sana'a Ka Ke? Uwa Tagari ta ki Karbar Motar da 'Danta ya Gwangwaje ta da Ita

Wacce Sana'a Ka Ke? Uwa Tagari ta ki Karbar Motar da 'Danta ya Gwangwaje ta da Ita

  • Wata mata 'yar Najeriya tayi watsi kyautar motar da 'danta ya dankara mata ranar zagayowar haihuwarta, inda ta nuna damuwarta game da yadda yake samun kudi
  • Matar tayi mamakin yadda 'dan nata wanda har yanzu yake jami'a ya iya dankara mata wannan kyautar ta makuden miliyoyi
  • A faifan bidiyo wasu mutane sun yi imani cewa shiri ne kawai, inda ta tarwatsa balan-balan din da ke kan motar yayin da ta umarce shi da ya 'bace mata daga gani

Wata mata 'yar Najeriya ta ba 'danta, abokansa da masu amfani da yanar gizo da dama mamaki bayan tayi fatali da kyautar motar da ya bata ranar zagayowar haihuwarta.

Uwa tagari
Wacce Sana'a Ka Ke? Uwa Tagari ta ki Karbar Motar da 'Danta ya Gwangwaje ta da Ita. Hoto daga Maria Ude Nwachi
Asali: Facebook

An dauki guntun bidiyon da Maria Ude Nwachi ta wallafa a shafinta na Facebook.

Ta zargi matashin da zama 'dan damfarar yanar gizo gami da kokawa da yadda yayi kokarin amfanin da ita wajen tsafi ta hanyar bata kyautar mota.

Kara karanta wannan

Jama'a Sun Yabawa Kwandastan Motan da ya Dire daga Bas, Ya Tafi Nemawa Fasinja Mara Lafiya Ruwan Sha

Duk iya kokarin da matashin da abokansa suka yi wajen gamsar da ita karbar motar, hakan bai hanata kin amincewa gami da umartarsa da ya fice mata da ita daga ganinta yayin da ta farfasa balan-balan din da aka kawata motar dasu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarta, har yanzu shi dalibi ne a jami'a wanda bai da aikin yi saboda haka bashi da kudin siyan wannan dankareriyar motar.

"Kai kawai dalibi ne. Wanne aiki ka ke yi?"

- Ta ce da shi.

Yayin da wasu masu amfani da yanar gizo ke jinjinawa matar, wasu sun yi tunanin shirya hakan aka yi, musamman yadda tayi ta kiran 'dan da ta haifi da 'da na.'

Sai dai, Legit.ng ta kasa tabbatar da ingancin faifan bidiyon har zuwa lokacin da aka tattara wannan rahoton.

Martanin 'yan soshiyal midiya

Kara karanta wannan

Tuntuni Nake Kuka: Budurwa a Bidiyo ta Labarta Yadda Mahaifiyarta ta Watsa Mata Rayuwarta

Vivian Okenna Amanda Chukwuani ta ce:

"Iyaye mata nawa ne za su iya haka a yau?...sako ya isa inda ake so, duk da yayi kama da shiri iyaye kadan za su iya haka a yanzu."

Ifeanyichukwu Ugwuoke ya ce:

"Wasan kwaikwayo. "Meye kuma " 'da na"? Ba ta ga madubin motar da zata tarwatsa ba, sai balan-balan take farfasawa. Sai fa."

Desmart Kalumalu Orakaeze ya ce:

"Wasan kwaikwayo bai yi kyau ba. Shi 'dan bai da suna?! Wacce uwa ce ke kiran 'dan ta da 'da na? Ba ma Ochuko ko Chukwuebuka ko Bamidele ko Musa ba?"

Abazie Nwachimereze Juliet ta ce:

"Lafiya lau, motar da ba tsada gareta ba kuma kai dalibi ne. Wannan shi ne yadda uwa ta gari za tayi. Na jinjina wa wannan jarumar uwar."

Igwe Gucci T ya ce:

"Wannan uwar ta gari ce, kuma ina alfahari da ke hajiya. Idan kowacce uwa za ta tuhumi yadda 'ya'yanta suke samun kudi, a kalla 'yan damfarar yanar gizo, Aristi da sauransu kashi 50 za su daina."

Kara karanta wannan

Bidiyo: Matar Aure ta Koka da Yadda Ta Koma Kamar Gardi Bayan ta Samu Juna Biyu, Jama'a Sun Kwashi Nishadi

Chinonyerem Queen ta ce:

"Abun dariya kaina wasan kwaikwayo inukwam 'da na mai mamakon nwam, da kin kira shi bdaymake sai muce da gaske ne."

Daliba ta kafa sana'a da kudin makarantarta

A wani labari na daban, wata budurwa 'yar Najeriya ta bayyana ofishinta bayan da ta tattara kudin makarantarta ta kafa sana'a.

Tace taka kwance a gado dabara ta fado mata kuma ta kwashi kudin makarantarta ta kafa wurin siyar da abinci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel