Bidiyon Yadda Budurwa ta Sukurkuce Tare da Canza Kamanni Saboda Juna Biyu

Bidiyon Yadda Budurwa ta Sukurkuce Tare da Canza Kamanni Saboda Juna Biyu

  • Wata mata dake dab da haihuwa ta bayyana hotunan yadda take kafin samun juna biyun da yadda ta koma kamar kurar tashe
  • Canjin da ya bayyana karara yayi yawo a dandalin TikTok inda masu amfani da yanar gizo suka yi tsokaci game da abun da ake fuskanta kafin kawo rai duniya
  • 'Yan soshiyal midiya sun bar martani masu ban dariya yayin da mutane suka yarda da maganar matar wacce ta damu da yadda ta koma

Wata mata ta bayyana yadda ta koma kamar kurar tashe bayan samun juna biyu. Matar tayi bidiyo ne don nunawa jama'a yadda juna biyu ya canza mata kamanni gaba daya.

Mai Ciki
Bidiyon Yadda Budurwa ta Sukurkuce Tare da Canza Kamanni Saboda Juna Biyu. Hoto daga TikTok beegulethu_.
Asali: UGC

Masu amfani da yanar gizo sun sha mamakin ganin yadda halittarta ta canza gaba daya.

Mutane a martanin da suka yi basu duba mata ba, inda suka kwashi nishadi da hallitar da ta zama.

Kara karanta wannan

Kyakkyawar Budurwa Ta Auri Mai Nakasu Bayan Ta Rabu Da Attajirin Saurayinta

Mai amfani da kafar TikTok din, @beegukethu ta nunawa jama'a yadda juna biyu ke canza halittar mutum.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Matar ta nuna yadda juna biyun ya maida mata fuska kamar ba ita ba.

A wallafar da tayi, ta rubuta:

"Abun dariyar shi ne ban san ina da juna biyu ba a bidiyon farko, wannan jinjirar tana gaba dani fa!"

Masu amfani da kafar TikTok sun yi martani game da yadda juna biyun ya canza halittar matar.

Sai dai, masu amfani da yanar gizon basu kyale matar haka nan ba, sun zolaye ta matuka.

Kalla cikakken bidiyon:

Martanin jama'a

Thembinkosi Dube773 yayi tsokaci:

"Kada ki kara yi."

Allthingssimone yayi tsokaci:

"Amma dai hancin ya koma daidai kuwa, saboda wannan ne babban abun da nake ji wa tsoro."

Kara karanta wannan

Yadda Wasu Suka Raba Amarya da Ido Daya a Wajen Shagalin Bikinta a Kano, An Kama Mutum Biyu

Skylar ta ce:

"Rai na ya bar jikina."

Jessica_Jessi tayi tsokaci:

"Ta yaya?"

Ituselolo tayi tsokaci:

"Me ya faru?"

Lin_Lin yayi tsokaci:

"Manyan abubuwan da ke firgitani su nake gani a wannan kafar."

choco_latte tayi tsokaci:

"Wannan sai dai mahaifin saboda hakan ba zai yuwu ba."

Karabelo Monyatso yayi tsokaci:

"Mata?"

Budurwa ta kafa kasuwanci da kudin makarantarta, ya tumbatsa cikin shekara uku

A wani labari na daban, wata budurwa ta bayyana yadda ta kafa katafaren kasuwancin abinci da kudin makarantarta yayin da ta ke daliba a jami'a.

Tace kwance ta ke kan gado lokacin da dabarar ta fado mata, kuma ta kwashi kudin makarantarta ta zuba a kasuwancin, ba ta yi nadama ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel