Bayan Shekaru 3, Budurwar da ta Narka Kudin Makarantarta a Kasuwanci, Ta Bayyana Ofishinta

Bayan Shekaru 3, Budurwar da ta Narka Kudin Makarantarta a Kasuwanci, Ta Bayyana Ofishinta

  • Ba tare da wani bata lokaci ba, wata matashiyar budurwa ta bi wata dabara da ta fado mata yayin da ta ke kwance kan gado a makaranta shekaru uku da suka gabata
  • A yau, wannan dabarar da ta aiwatar da kudin makarantar ta na jami'ar jihar Legas, LASU na wancan lokacin ya haifar mata da 'dan mai idanuwa
  • Budurwar cike da farin ciki ta hanzarta zuwa soshiyal midiya don bayyana irin albarkar da ta samu a kasuwancinta yayin da ta bayyana kalubalenta a jihar Legas

Wata budurwa 'yan Najeriya ta je soshiyal midiya don bayyana kyakyawan wurin aikinta wanda ta kafa shekaru uku da suka wuce da kudin makarantar ta.

Budurwar da ta kammala karatunta na digiri daga jami'ar jihar Legas, ta bayyana yadda tana kwance kan gadonta a makarantar wata rana dabarar fara kasuwancin abinci ya fado mata.

Kara karanta wannan

Ina Jin Yaruka 3: Budurwa Yar Abuja Da ke Kwasan Albashi Rabin Miliyan Tana Neman Mijin Aure, Ta Fadi Irin Wanda Take So

Ofishin Budurwa
Bayan Shekaru 3, Budurwar da ta Narka Kudin Makarantarta a Kasuwanci, Ta Bayyana Ofishinta. Hoto daga @Ade_authority
Asali: UGC

Tace ta hanzarta bin dabarar da ta fado mata babu wani bata lokaci kuma ta kaddamar da ita da kudin makarantar ta.

Ta kwatanta tafiyar kasuwancinta da tafiya mafi tsauri da ta taba yi a rayuwarta. Wasu kalubalen da ta fuskanta wurin kafa wurin sabon kasuwancinta sun hada da rashin kyan titi, 'yan daba da tsaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sabuwar 'yar kasuwar tace a gaskiya kasuwanci ba wasan yara bane. Tuni jama'a da yawa suka dinga mata Allah sam barka tare da taya ta murnar wannan nasarar.

Ga wallafarta a Twitter:

Soshiyal midiya tayi martani

@Lamide__O yace:

"Na taya ki murna, Ade. Allah karo nasara.
"Tsakanin lokacin da za ta yi ritaya, ina ga sauran jama'a sun fara gadon filayen bogi daga iyayensu. Duk wadannan biyan da ake yi ana yin su ne ta yadda duk wata dabarar kasuwancinka za ta bace."

Kara karanta wannan

A Wannan Ga'bar Ina Bukatar Taimako: Wata Mata Ta Koka Bayan Ta Kama Diyarta Budurwa a Dakin Danta, Ta Saki Bidiyo

@Oladunni_mike yace:

"Ina ki ka ga wanna kudin? Kafa kasuwanci a Najeriya ba na mai rashin juriya bane. Na taya ki murna CEO. Kin cancanci yabo mai yawa."

@thefestusakande yace:

"Babban karfafa guiwa Ade. Tabbas na yadda da ke, kasuwanci yana da wuya."

Kun tafka abun kunya, fasto ga mambobin cocinsa

A wani labari na daban, wani fasto yayi wa mambobin cocinsa tatas bayan da ya zargesu da matsolancin saka sadakar N100 da N20.

Faston yace abun nkunya ne mutum ya saka irin wannan kudin duk da tsadar man fetur da ake yi tunda yana siyan a kalla ita 20 ta fetur a kowacce rana.

Ya tabbatarwa da wadanda ke cikin cocin cewa, albarka na iya zuwa ta tsallake su ta samu wanda ke wajen cocin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel