Yadda Kwandasta ya Dira daga Mota Don Siyasa Fasinja Mara Lafiya Ruwa, Jama'a Sun Yaba

Yadda Kwandasta ya Dira daga Mota Don Siyasa Fasinja Mara Lafiya Ruwa, Jama'a Sun Yaba

  • Wani kwandastan mota ya samu jinjina daga masu amfani da kafar sada zumuntar zamani bayan nuna irin jinkan da yake da shi
  • Kwandastan mai matukar kirki ya kula da yadda wata fasinja mace bata da lafiya, bayan inda yayi iya kokarinsa don taimaka mata
  • Lola Okunrin, wacce ta wallafa labarin da Twitter, ta ce kwandastan ya hanzarta sauka daga motar Bus din don nemowa fasinjar ruwa

Wani kwandastan motar bus ya narkar da zukatan masu amfani da yanar gizo bayan ya taimakawa wata fasinja mara lafiya da ke cikin motar.

Yayin da bus din ta tashi, kwandastan ya lura da yadda matar ke zaune a rakube cikin bus din bata da lafiya.

Ya hanzarta tsaida motar, inda fasinjoji suka fara mamakin inda ya je.

Bayan wani dan lokaci, kwandastan ya dawo da ruwa gami da mikawa fasinjar mace. Ya ce ya lura da yadda bata jindadi hakan yasa ya yanke shawarar taimakonta.

Kara karanta wannan

Daga TikTok: Matashi ya tattara N1m, ya tallafawa wata tsohuwa da ya gamu da ita a titi

Yayin wallafa labarin a Twitter, mai amfani da kafar mai suna Lola Okunrin ta ce:

"A cikin mota da na hau zuwa Ketu yanzun nan. Kwandastanmu ya hanzarta sauka daga ciki a tashar motar Estate ba tare da fada mana inda zai je ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Mun fara nemansa ke da wuya, direban har ya fusata, fasinjoji sun hassala kawai ya dawo da ruwan gora mai sanyi gami da mikawa ga matar da tafi kowa korafi.
"A cewarsa, a iya tafiyar da aka yi, ya lura da yadda bata da lafiya, hakan yasa ya hanzarta zuwa nemo mata ruwa yadda zata sha don samun sassauci.
"Tabbas, matar na fama da ciwon kai, gayen ya gane hakan, inda yaje nemo mata ruwa don ta zuba a kanta. Ara mi bu mo aso. Zuciyata ta narke❤️zukatanmu sun narke.

Kara karanta wannan

Mata Mai Shekaru 47 Tayi Kira ga Gwamna da Yazo Ya Karba ‘Dan da Ta Haifa Masa Bayan Cikin da ya Dirka Mata ya Tsere

"Wannan nuna damuwar ya tabani❤️."

Martanin 'yan soshiyal midiya

AY Peter Obi ya rubuta:

"Wadanda suka fi munin hali cikinsu suma suna da nasu kyakyawan halin. Da yawanmu da suka tashi a Legas sun san kyawun halin yaran anguwa a wani bangaren."

Oginni Taiwo ya kara da cewa:

"Eh. Akwai wata rana da naji kishi kuma ba na da canjin siyan ruwa. Na tsaya kusa da inda ake sai da ruwan, ina kokarin hutawa yayin da nake kallon ruwan da dayan idona.Lokacin da wannan gayen yazo, ya siyama kansa ruwa da ni. Ya tafi kafin in masa godiya."

Ronaldo na neman mai girki a sabon gidansa, zai dinga biyan N2.5m a wata

A wani labari na daban, shahararren 'dan kwallon kafa, Cristiano Ronaldo, ya bayyana cewa yana neman kuku a sabon gidan da yake ginawa a Portugal.

Zai dinga biyan mai girkin N2.5 miliyan a kowanne wata amma girkin kasar Japan ya ke bukata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel