Bidiyon Budurwa Tana Rafsar Kuka, Ta Bayyana Yadda Mahaifiyarta ta Bata Mata Rayuwa

Bidiyon Budurwa Tana Rafsar Kuka, Ta Bayyana Yadda Mahaifiyarta ta Bata Mata Rayuwa

  • Wata budurwa 'yar Najeriya cikin kuka ta bayyana yadda mahaifiyarta ta tarwatsa rayuwarta da yadda ta raineta
  • A cewarta, iyayenta sun dauketa kamar wata babba tun lokacin da take da shekararta 10 a duniya tana 'yar karamar yarinya
  • Ta labarta irin musgunawar da tayi fama da shi wurin mahaifinta da abubuwan da suka tilasta tayi a baya

Wata budurwa 'yar Najeriya ta zargi mahaifiyarta da tarwatsa mata rayuwa, inda ta ce an musguna mata a lokacin da take karama.

Budurwa
Bidiyon Budurwa Tana Rafsar Kuka, Ta Bayyana Yadda Mahaifiyarta ta Bata Mata Rayuwa. Hoto daga TikTok/(@tambile_)
Asali: UGC

A wani bidiyon TikTok, budurwar ta labarta yadda aka taso da ita tana karama yayi sanadin lalacewar alakarta a yanzu.

Ta bayyana yayin da take ta sharbar kuka tun safe bayan wata hatsaniya ta shiga tsakaninta da mahaifiyarta kan irin musgunawar da aka mata tana karama. Ta bayyana yadda aka taba mata dukan kawo wuka tana 'yar yarinya.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Matar Aure ta Koka da Yadda Ta Koma Kamar Gardi Bayan ta Samu Juna Biyu, Jama'a Sun Kwashi Nishadi

A kalamanta:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Tun safe nake sharbar kuka bayan wata hatsaniya tsakanina da mahaifiyata 'yar Najeriya game da irin kuncin rayuwar ita da mahaifina suka saka ni. Yadda suka saba jibgata kamar bakuwar karya lokacin ina karama.
"Ina zuwa wurin atisaye ne saboda saukar da wahalar da na sha."

Yadda akewa babba haka aka mata tana karama, yayin da ta tuna yadda iyayenta suka horar da ita kamar babba sanda take 'yar karama.

"Sun horar da ni kamar babba lokacin ina kankanuwa. Ni ke kula da kannaina, in musu wanka gami da kai su makaranta. Ni na raini kannena ina shekara 10."

Budurwar da ta tattara komatsanta ta bar gida tana shekara 17 ta koka game da yadda kanwarta ta sha wahala shekaru da suka shude.

"Nayi kokarin mata magana kan haka a yau saboda irin haka take yi ma 'yar uwata. Na fada mata, a wannan matakin, yarinyar nan za ta iya barin gidan. Za ku rasa ta."

Kara karanta wannan

Allah mai Baiwa: Bidiyon Makauniya da ta Kware Wurin Kitso da Daura Kallabi ta Kayatar da Jama'a

Game da yadda take taso da ita, a cewarta:

"Mahaifina ba zai taba daina jibgata ba har sai ya zubar min da jini. Na yafe masa amma ba zan taba mantawa ba."

Martanin jama'a

Awurama ya ce:

"Na tausaya miki irin abun da kika fuskanta, basu san irin kunci da radadin da suka saka mu ba, amma Ubangiji zai kula da ke zake masoyiya."

Asa Obodo oyibo ya ce:

"Irin wannan abun ne mahaifiyata ta min, amma yanzu ta fahimci me yasa, ita ma ba na kaunarta, kuma ba za ta iya bada abun da bata da shi ba, nima na yafe mata."

Steph ta ce:

"Ki numfasa! ki numfasa yar uwa!! Komai zai wuce. Kin yi daidai da kika fada mata yadda kika bar gida."

user4555079590985 ya ce:

"Ki yi hakuri da yadda aka cusguna miki. Yafe musu shi ne zai sa ki warke daga radadin. Ba hujja bace ki saka kan ki cikin wani hali da zaki ji radadin abun. Kina da matukar amfani!"

Kara karanta wannan

Budurwar da tayi Amfani da Kudin Makarantarta Shekaru 3 da Suka Wuce ta Kafa Kasuwancin Ban Mamaki

Fabbie Maurice ta ce:

"Na tsani kula da kannaina ina shekara 12, in tashi da sassafe kamar karfe 4:00 don shirya kalaci, yi musu wanka, dafa abincin dare bayan na dawo daga makaranta."

Yankin jihar Kwara da ke da kudinsu na daban a Najeriya

A wani labari na daban, yankin Ijara-Isin na jihar Kwara sun rungumi kudinsu na daban da suke amfani da shi a yankin wanda ba Naira bace.

Suna hada-hadar kasuwanci tare da sauran lamurran rayuwa da kudinsu nasu su kadai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel