Zamfara: 'Yan bindiga sun sace dalibai 5 na kwalejin lafiya da ke Tsafe

Zamfara: 'Yan bindiga sun sace dalibai 5 na kwalejin lafiya da ke Tsafe

  • 'Yan ta'adda dauke da miyagun makamai sun dire a garin Tsafe da ke jihar Zamfara inda suka sace daliban kwalejin lafiya 5
  • Majiyoyi sun sanar da cewa lamarin ya auku a sa'o'in farko na ranar Laraba inda 'yan bindigan suka sace daliban a gidajen da ke wajen makaranta
  • Yawan jami'an tsaron da ke kofar makarantar yasa 'yan ta'addan ba za su iya tunkarar wurin ba, dalibi 1 ya tsero daga hannun miyagun

Tsafe, Zamfara - 'Yan bindiga sun kutsa wani yanki na garin Tsafe kuma sun sace dalibai biyar na kwalejin kiwon lafiya da fasaha da ke tsafe a jihar Zamfara.

Kamar yadda Channels TV ta ruwaito, lamarin ya faru ne a sa'o'in farko na ranar Laraba. Wata majiya ta sanar da cewa miyagun 'yan bindiga dauke da miyagun makamai ne suka dira gidan daliban wanda yake wajen makaranta.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari na kashe N10bn a wata wajen ciyar da dalibai, FG

Zamfara: 'Yan bindiga sun sace dalibai 5 na kwalejin lafiya da ke Tsafe
Zamfara: 'Yan bindiga sun sace dalibai 5 na kwalejin lafiya da ke Tsafe. Hoto daga channelstv.com
Asali: UGC

Ya ce 'yan bindiga ba za su taba samun damar shiga makarantar ba saboda jami'an tsaron da ke kofar shiga.

Majiyar ta kara da cewa, daya daga cikin daliban da aka sace ya tsero daga hannun 'yan ta'addan. Har a halin yanzu jami'an tsaro ba su yi tsokaci kan lamarin ba.

Karin bayani zai zo muku daga baya...

Asali: Legit.ng

Online view pixel