Sarkin Musulmi Ya Yi Magana Kan Wa'adin Dena Karbar Tsaffin Naira, Ya Bukaci CBN Ta Kara Wa'adi

Sarkin Musulmi Ya Yi Magana Kan Wa'adin Dena Karbar Tsaffin Naira, Ya Bukaci CBN Ta Kara Wa'adi

  • Sarkin Musulmi Muhammadu Sa'ad Abubakar ya shawarci babban bankin kasa CBN ta sake duba batun dena karbar tsaffin naira a karshen Janairu
  • Sultan din ya yi wannan jawabin ne yayin da kwantrola na CBN a jihar Sokoto ya ziyarce shi a fadarsa don neman shawarwari
  • Sarkin musulmin ya ce mutanen karkara da dama ba su san an canja kudin ba kuma ta yi wu su ki karba idan an basu, ya kuma ce rashin tsaro na iya hana su kai kudinsu banki

Jihar Sokoto - Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa'ad Abubakar, ya shawarci babban bankin Najeriya, CBN, ta sake duba batun haramta cinikayya da tsaffin naira a ranar 31 ga watan Janairu, rahoton Daily Trust.

Da ya ke magana yayin tarbar Kwantrola na CBN a Sokoto, Dahiru Usman, da wasu manyan yan bankin a ranar Alhamis a fadarsa, sarkin ya ce har yanzu akwai wadanda ba su san da batun sauya nairan ba musamman a karkara.

Kara karanta wannan

2023: Ka Janye Idan Ka San Ba Ka Da Lafiya, Malamin Addini Ya Gargadi Yan Siyasa, Ya Ce Wani Jigo Zai Mutu

Suktan
Sarkin Musulmi Ya Yi Magana Kan Wa'adin Dena Karbar Tsaffin Naira, Ya Bukaci CBN Ta Kara Wa'adi. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce:

"Muna da mutanen da har yanzu ba su san cewa an sauya nairan mu ba. Za su iya kin karbar sabbin kudin idan an basu. Idan suka ga sabbin launin, za su yi tsammanin jabu ne.
"Ya kamata da CBN ta saka masu ruwa da tsaki a batun tunda farko.
"Muna da hanyoyin sadar da bayanai ga mutanen karkara domin kafar watsa labarai na zamani na yan boko ne. Da kunyi amfani da sarakunan gargajiya don isar da sakon amma ba ku tuntube mu ba, shi yasa muka yi shiru."

Rashin tsaro kallubale ne ga daukan kudi zuwa banki, Sarkin Musulmi

Sultan din ya kuma ce rashin tsaro kallubale ne da ke hana mutane daukan kudi mai yawa daga kauye zuwa banki a birane don ana iya musu fashi ko sace su a hanya.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Sabuwar Kungiyar ‘Yan Ta’adda Ta Bullo a Kudu, Sun Gindaya Sharadi Kafin Su Bari ayi Zabe

Daga nan ya yi tambaya:

"Me zai faru da irin wannan mutanen bayan wa'adin 31 ga watan Janairu ya cika?."

Ya kuma bayyana damuwarsa kan kayyade wa'adin cire kudi zai shafi yan kasuwa a kasar nan.

Jawabin Kontrolan CBN ga Sarkin Musulmi

Tunda farko, kwantrolan ya ce sun taho fadar ne domin su sanar da sarkin musulmin game da sauya nairan da e-bankin da kuma neman shawararsa.

Ya yi alkawarin cewa zai isar da sakon na Sultan zuwa hedkwatar bankin na kasa.

Hakazalika, wasu ma'aikatan babban bankin sun ziyarci wasu bankuna na kasuwanci a gari domin su tabbatar ana bada sabbin nairorin a ATM, kuma su wayar da kan mutane kan e-naira.

Wakilin Legit.ng Hausa ya zagaya injinin ATM na wasu bankunan kasuwanci da ke Dutse, babban birnin jihar Jigawa a ranar Juma'a da Asabar inda ya tarar da dandazon al'umma suna kokarin mayar da kudi da cire kudi a injinin ATM.

Kara karanta wannan

CBN Ya Zargi Wasu Bankuna Da Ɓoye Sabbin Takardun Naira Har N4.2bn A Wata Jihar Kudancin Najeriya

Wasu daga cikinsu da ya tattauna da su sun ce suna goyon bayan wannan kiran na sarkin musulmi na neman a tsawaita wa'adin dena karbar tsaffin takardun nairan.

Sun koka cewa babu bankuna a yawancin karkara da suka fito shi yasa suke zuwa birni don hada-hadar kudin suna mai cewa masu sana'ar POS duk da tsarin da CBN ta fito da shi na basu damar yi wa mutane musayar kudi bai wadata ba.

Wani dan kasuwa da ya ce sunansa Musa Shehu mazaunin Kiyawa ya ce:

"Gaskiya wa'adin da aka bayar ya yi kadan, musamman duba da cewa cikin yan kwanakin nan ne bankunan suka fara saka sabbin kudi a na'uarar ATM.
"Na ji dadin kiran da Sarkin Musulmi ya yi kuma ina fatan babban bankin zai saurari shawarar ya tsawaita mana wa'adin canja kudin.
"Wasu lokutan mutum zai yini a gaban banki yana kokarin cire kudi har yamma ba dole bane ya samu."

Kara karanta wannan

Tof fa: Bankuna sun Ssabawa CBN game da sabbin kudi, suna ta ba mutane tsoffin kudi a ATM

Wani mai Babangida Musa Takur wanda ya ce sana'ar sayar da kayan gine-gine ya ke yi a Dutse shima ya ce yana rokon a tsawaita wa'adin kamar yadda Sarkin Musulmi ya bukata.

A cewarsa:

"Gaskiya lokacin da aka bada bai isa ba, muna shan wahala sosai wurin cire kudi.
"Bisa alamu sabbin kudin ba su isa ba ko kuma akwai wasu shafaffu da mai da ake bawa kafin a fara kula wa da mu talakawa."

Mutane a gaban ATM a Dutse
Mutane da ke bin layin cire kudi a ATM a Jigawa.
Asali: UGC

Mutane a gaban ATM
Wasu mutane a gaban ATM a garin Dutse, Jihar Jigawa.
Asali: UGC

Legit.ng ta yi kokarin ji ta bakin jami'an wasu bankunan kasuwancin da ba su amince a fadi sunansu ba guda biyu, suna mai cewa ba za su iya tsokaci kan lamarin ba don ba a basu izinin magana ba.

"Muna iya kokarin mu don wadatar da kwastomomin mu da sabbin kudaden kuma muna fatan idan aka yi hakuri kowa zai samu kudin."

Asali: Legit.ng

Online view pixel