Zaben 2023 Ba Na Yan Takara Marasa Koshin Lafiya Bane – Primate Ayodele Ya Yi Gargadi

Zaben 2023 Ba Na Yan Takara Marasa Koshin Lafiya Bane – Primate Ayodele Ya Yi Gargadi

  • Shaharren malamin addini a Najeriya, Primate Elijah Ayodele, ya shawarci yan siyasa da basu da isasshen lafiya da su hakura su janye daga neman takara
  • Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, ya ce aikin shugabanci ba na wanda bai da isasshen lafiya bane
  • Faston ya kuma yi hasashen cewa Najeriya za ta yi babban rashi na wani shahararre cikin gwamnoni, sanatoci da yan majalisa da za a zaba

Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele, ya bayyana cewa zaben shugaban kasa na 2023 ba na wadanda basu da cikakken lafiya bane.

Malamin addinin wanda ya bayyana hakan a ranar Lahadi, 22 ga watan Janairu, ya ce aikin na bukatar mutum mai jini a jika, Nigerian Tribune ta rahoto.

Primate Ayodele
Zaben 2023 Ba Na Yan Takara Marasa Koshin Lafiya Bane – Primate Ayodele Ya Yi Gargadi
Asali: Original

Primate Ayodele ya kuma caccaki manyan yan takara a zaben shugaban kasa mai zuwa kan rashin yin magana kan matsalolin da kasar ke fuskanta a kamfen dinsu.

Kara karanta wannan

Peter Obi Ya Fallasa Wani Babban Sirri 1 Game Da Kansa Da Abokin Takararsa Ahmed-Datti

A wata sanarwa dauke da sa hannun kakakinsa, Osho Oluwatosin, Primate Ayodele, ya bayyana cewa yan takarar na cewa za su yi komai amma basu yi magana game da yadda za su yi shi ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yan Najeriya za su ci gaba da fuskantar matsaloli idan ba a yi hattara ba

Ya ambaci cewa kasar na fuskantar matsalolin tattalin arziki, rashin tsaro da na ilimi amma yan takarar basu mayar da hankali wajen magance wadannan a kamfen dinsu.

Ya nuna fargabar cewa ba lallai ne yan Najeriya su rabu da matsalolin da suke fsukanta ba a yanzu saboda yan takarar basa magana a kansu.

Ya ce:

"Yan takarar shugaban kasar na neman kuri'u ne kawai, basu fadi hanyar magance matsaloli ba, suna dai cewa za su iya yin komai wanda ba mai yiwuwa bane.
"Mun tabbata muna tunkarar zabe ne saboda wadanda muke so su wakilce mu basu fito sun fada mana yadda za su magance wadannan matsalolin da muke fuskanta ba. Watakila mu ci gaba da fuskantar wadannan matsalolin a gaba sabida basa magana kan wadannan matsalolin."

Kara karanta wannan

Rudani: Dole a dage zaben 2023 saboda wasu dalilai, malamin addini ya magantu

Har ila yau, Primate Ayodele, ya gargadi INEC a kan kada su tsorata game da lamarin BVAS, yana mai cewa bai kamata INEC ta yi sanya ba saboda zaben mai muhimmanci ne, rahoton Independent.

Wani shahararren dan siyasa da za a zaba zai mutu

Ya kuma bayyana cewa wani shahararren mutum a cikin gwamnoni, sanatoci da yan majalisar wakilai da za a zaba zai mutu.

Faston ya kuma shawarci wadanda basu da isasshen lafiya da su janye daga zaben don kula da lafiyarsu.

"Tsorona a zabe mai zuwa shine cewa Najeriya za ta rasa wani babban mutum a cikin gwamnoni, sanatoci da yan majalisar wakilai da za su zaba. Idan ka san baka da lafiya, je ka kula da kanka, zabe ba shine abun da kake bukata ba."

Korar masu biyayya ga G5 ba zai amfani PDP da komai ba - Wike

A wani labari na daban, Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya dauki dumi a kan korar wasu jiga-jigan PDP masu biyayya ga tsaginsa.

Wike ya ce za su sanya kafar wando daya da shugaban babbar jam'iyyar adawar na kasa, Iyorchia Ayu gabannnin zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel